| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
DSS ta saki mutumin da aka tsare saboda zargin alaƙa da Boko Haram bisa kuskure, ta biya shi diyya
Jaridun Nijeriya sun rawaito cewa Shugaban DSS ne ya bayar da umarnin sakin manomin, Nura Idris, wanda kuma makiyayi ne daga Karamar Hukumar Soba ta jihar Kaduna, yayin da ake ci gaba da nazari kan batutuwan waɗanda aka tsare ba bisa ƙa'ida ba.
DSS ta saki mutumin da aka tsare saboda zargin alaƙa da Boko Haram bisa kuskure, ta biya shi diyya
DSS Nigeria / Others

Hukumar Tsaron Farin Kaya ta Nijeriya (DSS) ta saki wani makiyayi daga jihar Kaduna, kuma ta wanke shi daga zargin alaƙa da ƙungiyar Boko Haram, sannan ta biya shi diyyar naira miliyan uku.

Jaridun Nijeriya sun rawaito cewa Shugaban hukumar DSS Oluwatosin Adeola Ajayi ne ya bayar da umarnin sakin manomin, Nura Idris, wanda manomi ne kuma makiyayi daga Karamar Hukumar Soba ta jihar Kaduna, yayin da ake ci gaba da nazari kan batutuwan waɗanda aka tsare ba bisa ƙa’ida ba.

Majiyoyin tsaro sun ce binciken cikin gida na DSS ya tabbatar da cewa babu wata alaƙa tsakanin Nura da ‘yanta’addan Boko Haram.

Majiyoyin sun ce wata hukumar tsaro ce ta kama Nura a watan Yunin 2024 a Suleja, Jihar Neja, kafin daga bisani aka mika shi ga hukumar DSS bisa zargin yana da alaƙa da ta’addanci.

Bincike da Diyya

Bayan cikakken bincike kan lamarinsa, DSS ba ta samu wata hujja da ke danganta shi da ta’addanci ba.

Bisa haka ne shugaban hukumar ya umarci a sake shi nan-take, tare da amincewa a ba shi naira miliyan 3 a matsayin diyya don tallafa masa wajen komawa cikin iyalansa da kuma sake gina rayuwarsa, tare da alƙawarin ƙarin taimako don ya sake dogaro da kai.

Da yake magana bayan an sake shi, Nura Idris ya nuna godiyarsa ga hukumar DSS, inda ya bayyana hakan a matsayin wani abu da zai sauya rayuwarsa, sannan ya yaba da kyakkyawar kulawar da ya samu yayin da yake tsare, a cewar jaridun Nijeriya suna ambato majiyoyin tsaro.

Baya ga Nura, hukumar ta DSS ta kuma yi nazari kan tuhume-tuhume fiye da 30 tare da biyan diyyar sama da naira miliyan 300 ga mutanen da aka tsare ba bisa ka’ida ba.

Daga cikin mutanen da aka saki akwai waɗanda a baya aka zarge su da alaƙa da haramtacciyar Ƙungiyar Fafutuƙar Kafa Ƙasar Biafra (IPOB) da sauran ƙungiyoyin ta’addanci, bayan bincike ya tabbatar da ba su da laifi.

DSS ta bayyana cewa, wannan shiri yana nuna himmarta wajen daidaita tsaron kasa tare da kare haƙƙin ‘yanƙasa, yayin da take ƙara ƙarfafa amincewar jama’a ga cibiyoyin tsaro na ƙasar.