Ɗanwasan gaban Coventry City, Taiwo Awoniyi, zai maye gurbin ɗanwasan gaban Galatasaray Victor Osimhen a cikin jerin sunayen ‘yanwasan tawagar Nijeriya ta Super Eagles yayin da aka buɗe sansanin horas da ‘yanwasan tawagar da za su taka leda a wasannin neman shiga Gasar Kofin Afirka da za ta yi a watwan Satumba.
Nijeriya za ta kara da Madagascar ranar 25 ga watan Satumba yayin da za ta kece reni da da Guinea-Bissau ranar 29 ga watan Satumba.
Ranar Lahadi ne dai tawagar ta Super Eagles ta bayyana cewa Victor Osimhen ba zai iya buga wasannin neman shiga Gasar Kofin Afirkan ba.
A wata sanarwar da ta wallafa a shafinta na X, tawagar ta ce ba zai iya buga wasannin ba saboda ya samu ya ci gaba da warkewa daga raunin tsokar jiki da ya ji.
Wannan shi ne karon farko da Awoniyi zai koma buga wasa wa Super Eagles tun shekarar 2024.
Kazalika tawaar ta Super Eagles ta bayyana a shafinta na X cewa ranar Litinin ne za a buɗe sansanin horas da ‘yanwasan tawagar gabannin wasannin inda ta tambayi mutane wa suke ganin zai fara shiga sansanin.
Nijeriya dai ita ce ta zo ta uku a Gasar Kofin Afrika ta 2025 da aka buga a ƙasar Maroko.






















