Za a yi karon-battar taurari a wasan Faransa da Sifaniya na zagayen semi-fainal
WASANNI
3 minti karatu
Za a yi karon-battar taurari a wasan Faransa da Sifaniya na zagayen semi-fainalMasu bibiyar gasar suna ganin Faransa ce ta fi kowace tawaga ƙarfin a fannin ‘yanwasan gaba, yayinda Sifaniya take da ƙarfin masu tsaron baya.
Faransa ce ta lashe Kofin Duniya a 2018, yayin da Sifaniya ta lashe a 2010.

A maraicen Talatan nan za a barje gumi tsakanin jaruman Turai, Sifaniya da Faransa a wasan dab da na ƙarshe a gasar Kofin Duniya da za a kammala ƙarshen watan nan a Amurka, Canada, da Mexico.

Wasan dai zai haɗa manyan taurarin ƙwallo na Turai da ma duniya bakiɗaya, kasancewar akwai gwarazan kyautar Ballon d’Or mafi kusa, wato na 2025, Ousmane Dembele na Faransa, da na 2024 Rodri na Sifaniya.

Baya ga su akwai taurarin da a bana suke kangaba wajen cancantar lashe kyautar ɗanƙwallo na duniya, wato Kylian Mbappé daga Faransa, da kuma matashin ɗanwasa, Lamine Yamal daga Sifaniya.

Ƙasashen Faransa da Sifaniya, da ma sauran ƙasashe biyu da ke buga ɗayan wasan samifainal na gasar, wato Ingila da Argentina, sun kasance ƙasashe huɗu da ke kangaba a gwanintar ƙwallo a jadawalin hukumar FIFA tsawon kusan shekaru biyu kenan.

Wasan zai gudana a filin wasa na Dallas Stadium da ke garin Arlington, da ke jihar Texas ta Amurka, kuma yana cikin wasannin da suka fi ɗaukar hankalai a jimillar wasanni kusan 100 da aka buga zuwa yanzu a gasar.

Fainal kafin fainal

Kamar yadda aka ambato kocin tawagar Faransa yana faɗa ranar Litinin, akwai da yawa masu bibiyar gasar ta bana da ke cewa wasan na yau tamkar wasan ƙarshe ne na gasar saboda armashinsa, duk da cewa, a zahiri shi ne na ukun ƙarshe.

"[Wasan Faransa da Sifaniya] zai iya zama wasan ƙarshe kafin na ƙarshe na Kofin Duniya, kamar yadda wasa tsakanin Argentina da Ingila zai iya zama tamkar na fainal. Mu duke ne ke kangaba a tawagogin ƙasashe," in ji kocin Sifaniya, Luis de la Fuente.

Masu bibiyar gasar suna ganin Faransa ce ta fi kowace tawaga ƙarfin a fannin ‘yanwasan gaba, yayinda Sifaniya take da ƙarfin masu tsaron baya.

A tarihin gasar na baya-bayan nan, Faransa ce ta lashe kofin a 2018, yayin da Sifaniya ta lashe a 2010, duka da cewa ita Sifaniya wannan ne karonta na farko na ɗaga kofin, wanda abokiyar karawarta ta lashe sau biyu.

Wani fifiko da Faransa take da shi, shi ne tawagar ta fito fainal a dagsanni biyu na baya-bayan nan, duka ƙarƙashin koci Didier Deschamps.

Dakarun tawaga

Ban da Kylian Mbappé da Ousmane Dembélé, a gaban tawagar akwai dakaru kamar Michael Olise. Mbappe ne yake kangaba a a zura ƙwallaye da ƙwallo takwas, kankankan da Lionel Messi.

Haka shi ma Dembélé yana da ƙwallo biyar zuwa yanzu a gasa, sannan shi kuma Olise shi ya fi kowa tawan ba da tallafin cin ƙwallo, har sau biyar zuwa yanzu.

Sauran taurarin ‘yanwasan Faransa sun haɗa da Mike Maignan, Jules Koundé, William Saliba, Theo Hernández, Aurélien Tchouaméni, Adrien Rabiot, Marcus Thuram, Désiré Doué, Bradley Barcola, Randal Kolo Muani, Eduardo Camavinga, Ibrahima Konaté, da sauransu.

A ɓangaren Sifaniya, bayan buga wasanni shida zuwa yanzu, sau ɗaya kacal aka zura mata ƙwallo shi ma a matakin kwatafainal ne a hannun belgium. Kuma idan har ta lashe kofin a haka, to za ta kafa tarihin mafi ƙaranci ƙwallon da aka ci zakaru.

Tawagar ta Sifaniya na alfahari da gwarzon ƙwallon duniya na 2024, Rodri, da matashin tauraro Lamine Yamal, wanda ya cika shekaru 19 ranar Litinin da ta gabata.

Sauran taurarin ‘yanwasan Sifaniya sun haɗa da Pedri, Pau Cubarsí, Marc Cucurella,Dani Olmo, Mikel Oyarzabal, Mikel Merino, Nico Williams, Ferran Torres, Fabián Ruiz, David Raya, da sauransu.

Rumbun Labarai
Barcelona ta miƙa ƙoƙon-bara wajen masu zuba jari don neman kuɗin gyaran filin wasa
Turkiyya ta kuma lashe kofin gasar volleyball ta mata ta nahiyar Turai
An yanke wa Tiger Woods hukuncin haramcin tukin mota tsawon shekaru 5 saboda tuki cikin maye
Muhimman batutuwa game da ritayar Messi daga tawagar Argentina
Sakon Lionel Messi na yin ritaya daga buga kwallo a matakin kasa-da-kasa
"Jikina ya fara sakwarkwacewa" in ji Djokovic, bayan an fitar da shi daga Gasar US Open ta bana
Shugaban Hukumar Ƙwallon Ƙafar Nijeriya Musa Gusau ya yi murabus
Ɗanwasan Kamaru Carlos Baleba ya koma Man Utd daga Brighton
Habasha ta shiga takarar ɗaukar nauyin gasar AFCON ta 2028
An sayar da ƙwallon da Maradona ya ci Ingila da hannu a kan $3.35M
Ɗan Nijeriya Semi Ajayi ya taimaka wajen yi wa Man Utd dukan wulaƙanci a farkon Gasar Firimiya
Cristiano Ronaldo ya fara kakarsa ta 25 da ƙwallonsa na 977 a tarihin wasansa
EFCC ta fara binciken Hukumar kwallon kafa ta Nijeriya, NFF
Jamal Musiala na Bayern Munich ya ce farfaɗiyar sandarewa ce ke damun sa
Patrick Vieira, tsohon ɗanwasan Arsenal ya zama sabon kocin tawagar Senegal
Kamaru ta lashe Kofin WAFCON a karon farko bayan ta doke Malawi
Lionel Messi ya ɓarar da fenareti na uku a jere yayin da aka lallasa kulob ɗinsa da ci 4-1
Ɗanwasan Sifaniya da ya ci Gasar Kofin Duniya Ferran Torres ya koma PSG daga Barcelona
Hukumomin ƙwallon ƙafa 6 na Larabawa, ciki har da Qatar da Morocco na goyon bayan Infantino na FIFA
Shugaban Amurka Donald Trump ya gargaɗi FIFA a kan maye gurbin Infantino