| Hausa
DUNIYA
3 minti karatu
Tsarin kiwon lafiya a Gabas ta Tsakiya na fuskantar barazana yayin da rikici ke ƙara muni: WHO
Hare-haren da ake kai wa cibiyoyin kiwon lafiya da ‘yangudun hijira sun janyo cikas ga tsarin kula da lafiya da kuma barazana ga hanyoyin samar da kayayyakin lafiya na duniya, inda mata da yara ke cikin wadanda suka fi fuskantar hatsari, in ji WHO
Tsarin kiwon lafiya a Gabas ta Tsakiya na fuskantar barazana yayin da rikici ke ƙara muni: WHO
WHO ta ce hare-haren da ake kai wa cibiyoyin kiwon lafiya da ma'aikata na karuwa. / AP
6 awanni baya

Tsarin kiwon lafiya a sassan Gabas ta Tsakiya na fuskantar matsin lamba fiye da kwanaki 10 bayan barkewar rikici a yankin, in ji Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO).

A ranar Labara Hukumar ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce an kashe dubban mutane yayin da wasu da dama suka jikkata a tashin hankalin da ke ƙara tsananta a ƙasashe da dama na yankin

Fiye da mutum 1,300 ne suka mutu a Iran sannan kimanin 9,000 sun jikkata, a cewar rahotannin da WHO ta rawaito.

A Lebanon, akalla mutane 570 ne suka mutu yayin da fiye da 1,400 suka jikkata, Isra'ila kuma ta ba da rahoton mutuwar mutane 15 yayin da 2,142 suka jikkata.

Kazalika WHO ta ce, ana kara samun hare-hare kan cibiyoyin kiwon lafiya da ma'aikata.

"Waɗannan hare-haren ba wai kawai suna kashe rayuka ba ne, suna hana al'ummomi samun kulawa mai mahimmanci lokacin da suka fi buƙatarta," kamar yadda Darakta Janar na WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus ya bayyana a shafinsa na X, mallakin Amurka.

WHO ta yi gargaɗin cewa, rikicin ya haifar da ƙaruwar haɗarin lafiyar jama'a yayin da a ɓangare guda ya tilastawa mutane da dama barin gidajensu.

Fiye da mutane 100,000 daga Iran da kuma 700,000 a Lebanon ne suka rasa matsuguni, sannan da yawa suna rayuwa cikin mawuyacin hali tare da ƙarancin damar samun ruwa da muhalli mai tsafta.

Mutane masu rauni, musamman mata da yara, suna fuskantar ƙaruwar haɗarin rashin lafiya, in ji hukumar.

Ricikin na barazana ga hanyoyin samar da lafiya na duniya

Ayyukan kiwon lafiya na ci gaba da fuskantar barazana sakamakon rufe cibiyoyin kiwon lafiya.

A Lebanon, an rufe cibiyoyin kiwon lafiya 49 da asibitoci biyar saboda umarnin ƙwashe mutane, yayin da aka saka ‘‘dokar takaita’’ samun kulawa ta lafiya sosai a yankunan Falasɗinawa da Gaza da aka mamaye.

Kazalika rikicin ya shafi ayyukan isar da kayayyakin kiwon lafiya a duniya.

Haka kuma takunkuman da aka sanya na sararin samaniya ya kawo cikas ga hanyoyin samar da kayayyaki, wanda hakan ya haifar da cikas wajen isar da tarin muhimman kayayyakin kiwon lafiya da aka shirya kai wa mutane fiye da miliyan 1.5 a ƙasashe 25.

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta yi kira da a ɗauki matakin gaggawa daga dukkan bangarorin da ke da hannu a wannan faɗa.

Amurka da Isra'ila sun kai hare-hare kan Iran a ranar 28 ga Fabrairu, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane fiye da 1,300, ciki har da jagoran addinin musulunci na ƙasar Ali Khamenei, da kuma 'yan makarantar mata fiye da 150.

Tehran ta mayar da martani da hare-haren jiragen sama marasa matuki da makamai masu linzami kan Isra'ila, da Jordan, da Iraki, da kuma wasu ƙasashen yankin Gulf wadanda ke da sansanonin sojin Amurka a cikinsu.