| Hausa
NIJERIYA
3 minti karatu
Hukumar EFCC ta rufe asusun gwamnatin Jihar Osun kwanaki kaɗan kafin zaɓen gwamna
Wannan mataki ya ƙara tsananta takaddamar da ke tsakanin hukumar yaƙi da cin hanci ta tarayya da Gwamnatin Jihar Osun, wadda ke zargin EFCC da wuce iyakokin ikon da doka ta ba ta, tare da yunƙurin tsoma baki a harkokin jihar gabanin zaɓen gwamna.
Hukumar EFCC ta rufe asusun gwamnatin Jihar Osun kwanaki kaɗan kafin zaɓen gwamna
Gwamnatin Jihar Osun ta yi kakkausar suka ga matakin, tana mai cewa haramtacce ne kuma yana da manufar siyasa.

Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Nijeriya ta'annati ta ba da umarnin rufe wani asusun banki na Gwamnatin Jihar Osun da ke Kudu maso Yammacin Nijeriya, tana mai cewa ta gano nau’i na shige da fice na kuɗaɗen gwamnati da ake zargi, waɗanda ke da alaƙa da binciken da take yi kan zargin almundahanar kuɗi da ta kai kusan naira biliyan 11.

A wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X, EFCC ta ce ta fara wannan bincike ne tun a watan Maris na shekarar 2026, kuma ya shafi zargin karkatar da kuɗaɗen tallafi na kare muhalli da kuma na farfaɗo da na asusun rarraba kuɗaɗen gwamnatin tarayya wato FAAC.

 “Da a ce ba a samu shige da ficen kuɗaɗen da ba a amince da su ba da ba tun daga 2 ga Agustan 2026, da ba a ɗauki wannan matakin ba na bincike da dakatar da hana shige da ficen kuɗaɗe,” in ji sanarwar ta EFCC.

" Hukumar ta lura da manyan kuɗaɗe da ake turawa zuwa asusun wasu kamfanoni daban-daban, lamarin da ya sa ta gaggauta rufe asusun domin dakatar da wannan yanayi."

Wannan mataki ya ƙara tsananta takaddamar da ke tsakanin hukumar yaƙi da cin hanci ta tarayya da Gwamnatin Jihar Osun, wadda ke zargin EFCC da wuce iyakokin ikon da doka ta ba ta, tare da yunƙurin tsoma baki a harkokin jihar gabanin zaɓen gwamna.

EFCC ta ce ta riga ta yi wa jami'ai da dama tambayoyi a matsayin wani ɓangare na binciken, ciki har da Akanta Janar na jihar.

Gwamnatin Osun ta yi watsi da matakin

Gwamnatin Jihar Osun ta yi kakkausar suka ga matakin, tana mai cewa haramtacce ne kuma yana da manufar siyasa.

Gwamna Ademola Adeleke ya ce rufe asusun gwamnatin zai kawo cikas ga gudanar da ayyukan gwamnati a lokacin zaɓe, yana kuma zargin cewa an ɗauki matakin ne domin raunana gwamnatinsa gabanin zaɓen gwamna.

Babban Lauyan Jihar kuma Kwamishinan Shari'a, Oluwole Jimi-Bada, shi ma ya kalubalanci halaccin matakin, yana mai cewa EFCC ba ta da iko a kundin tsarin mulki na rufe asusun gwamnatin jiha ba tare da bin hanyoyin doka da suka dace ba.

Sai dai EFCC ta yi watsi da zargin cewa lokacin ɗaukar matakin yana da alaƙa da siyasa, tana mai cewa abin da ta yi ya zama wajibi ne domin kare dukiyar jama'a.

Hukumar ta ce:

"A ko da yaushe Hukumar tana bayyana cewa ba ta nuna bangaranci ko bambancin addini, illa dai tana aiki ne domin kare muradun 'yan Nijeriya baki ɗaya."

 

Rumbun Labarai
Majalisar Wakilan Nijeriya ta aika da ƙudirin kafa ’yansandan jihohi ga majalisun dokokin jihohi
Rikicin Amurka da Iran: NLC ta nemi gwamnatin Nijeriya ta ɗauki mataki bayan litar mai ta kai N1,500
Dakarun Nijeriya sun kubutar da mutane 31 da aka yi garkuwa da su a jihohin Katsina da Kebbi
Rundunar sojin Nijeriya 'ta kashe ‘yanta’addan Boko Haram da ISWAP fiye da 1000 a shekara ɗaya'
Samun ɗa namiji magaji ba ya gabana - Aliko Dangote
Rundunar 'yansandan Nijeriya ta yi gargaɗi game da yiwuwar kai hare-hare makarantu da wuraren ibada
Ana zargin ‘yanta’adda da kashe aƙalla mutum 13 a wasu hare-hare a Jihar Filato ta Nijeriya
'Yansandan Nijeriya sun kama mutum 262, sun kuma ceto 27 da aka yi garkuwa da su
An sace malamai shida da suka je taron addu’ar APC a Zamfara
Gwamnatin Nijeriya ta yi Allah wadai da kisan 'yan ƙasarta biyu a Afirka ta Kudu
FBI ta nemi haɗin kan EFCC don gudanar da bincike kan zargin karkatar da kuɗaɗen tallafin Amurka
Majalisar Dokokin Nijeriya ta dakatar da ziyarar aiki zuwa Afirka ta Kudu
Tinubu ya bai wa kowace 'yar tawagar ƙwallon kwandon Nijeriya dala dubu ɗari-ɗari
Mutum 511 sun kamu da cutar mashaƙo a Jihar Yobe a Nijeriya
Amurka ta aika sabbin kayayyakin soji Nijeriya
Zaben Nijeriya na 2027: Matakan Tinubu na rage talauci da alƙawarin Atiku na mayar da tallafin fetur
Jakadan Nijeriya ya ziyarci ’yan kasar 198 da ke gidan yari a Indiya
Mutane da dama sun mutu yayin da wasu ke asibiti bayan sun sha wani maganin gargajiya a jihar Ondo
Hukumar Shige da Fice ta Nijeriya ta kama wasu mutane da kudade da ake zargin kuɗin fansa ne
'Yansandan Nijeriya sun kama mutum biyu kan zargin kashe Danshagamu a Kano