| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Nijeriya: 'Yanbindiga sun kashe mutum 50 da garkuwa da wasu da dama a Jihar Zamfara
Harin ya faru ne a lokacin da ‘yanbindigar suka kutsa cikin ƙauyen Tungan Dutse a kan babura da tsakar dare, inda suka banka wa gine-gine wuta tare da harbin mazauna ƙauyen da suka yi ƙoƙarin tserewa.
Nijeriya: 'Yanbindiga sun kashe mutum 50 da garkuwa da wasu da dama a Jihar Zamfara
Matsalar tsaro a Nijeriya na ci gaba da taɓarɓarewa, musamman a yankin arewa maso yamma / Reuters
21 Fabrairu 2026

Aƙalla mutane 50 ne suka mutu yayin da aka yi garkuwa da mata da yara da dama a wani hari da aka kai wani ƙauye a Jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Nijeriya.

Harin, wanda ‘yan ta’adda da ake kira ‘yan bindiga a yankin suka kai, ya fara ne a daren Alhamis kuma ya ci gaba har zuwa safiyar Juma’a. Maharan da suka iso a kan babura sun banka wa gine-gine wuta tare da harbin mazauna ƙauyen Tungan Dutse da suka yi ƙoƙarin tserewa, kamar yadda Hamisu Faru, ɗan majalisar jiha, ya tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu a ranar Asabar.

“Tun daga daren Alhamis har zuwa safiyar yau babu wanda ya samu barci. Wasu mutane sun rasa ‘yan uwa uku daga cikin iyalansu,” in ji Faru ga Anadolu.

An shirya gawawwakin waɗanda suka mutu domin jana’izar gama-gari, inda aka lulluɓe su da farin likkafani a ranar Asabar. Har yanzu ba a tantance adadin mutanen da aka yi garkuwa da su ba, yayin da jami’an yankin ke ci gaba da ƙididdige waɗanda suka ɓace.

Halin tsaro a Nijeriya na ci gaba da taɓarɓarewa, musamman a yankin arewa maso yamma inda Jihar Zamfara take. Yankin ya daɗe yana fama da hare-haren ‘yanbindiga, sace-sace da kashe-kashe, lamarin da ya raba dubban mutane da muhallansu tare da jefa wasu da dama cikin haɗari.

Gwamnatin Nijeriya ta ɗauki wasu matakai domin magance matsalar, ciki har da tura sojoji da kuma haɗin gwiwa da ƙasashen waje kamar Amurka wajen samun tallafin fasaha da musayar bayanan sirri.

Sai dai har yanzu lamarin na ci gaba da kasancewa mai ƙalubale, sakamakon Ƙaruwar barazanar tsaro daga ƙungiyoyin ‘yan ta’adda.

 

Rumbun Labarai
Nijeriya na neman tallafin IMF da Bankin Duniya don rage tasirin yakin Iran kan tattalin arziki
Me ya sa hare-hare ke karu wa a Nijeriya duk da wanzuwar dakarun Amurka?
Rundunar Sojin Saman Nijeriya ta soma bincike kan zargin kisan fararen-hula a kasuwar Jilli ta Yobe
ADC ta taya sabbin shugabannin jihohi murna, ta tsayar da ranar 12 ga Mayu don rantsar da su
Gwamnatin Nijeriya ta ba da umarnin soke fasfo ɗin mutanen da suka janye daga kasancewa ’yan ƙasar
Man fetur yana tsada sosai, amma mu gode wa Allah halin da muke ciki ya fi na wasu ƙasashe – Tinubu
An gano gawarwaki 61 bayan harin ta'addanci a jihar Neja ta Nijeriya
Dakarun Nijeriya sun kashe 'yanta'adda tare da ƙwace makamai a Jihar Filato
Rundunar Sojin Nijeriya ta ce an kashe dakarunta a harin da Boko Haram ta kai hedkwatarsu a Borno
‘Gwarazan da ba za a iya mantawa da su ba’, Tinubu na juyayin kisan sojojin Nijeriya a harin Borno
Amurka ta bai wa jami'anta umarnin barin ofishin jakadancinta a Nijeriya saboda rashin tsaro a ƙasar
Aƙalla mutum 60 aka kashe a hare-hare daban-daban a arewa maso yammacin Nijeriya cikin mako guda
Bankin Duniya ya ce tattalin arzikin Nijeriya zai habaka a 2026
An mayar da 'yan Nijeriya 179 gida daga Libya
Babbar kotun Nijeriya ta ɗaure 'yanta'adda biyar
Dakarun Nijeriya sun kashe 'yanta'adda biyar, sun kama wanda ake zargi da garkuwa da mutane a Filato
Matatar Dangote ta ƙara man da take turawa ƙasashen Afirka yayin da yaƙin Iran ya katse jigilar mai
An buƙaci Nijeriya ta gyara yadda ake bayar da labaran rikice-rikice
An kama mutum biyar kan harbin bindiga ba bisa ƙa’ida ba da 'ya kashe' yarinya Maiduguri a Nijeriya
Abin da ya sa Kano Pillars ta lallasa Bendel Insurance da ci 4-0 — Koci