| Hausa
DUNIYA
2 minti karatu
Ana fargabar mutuwar 'yan ƙabilar Rohingya fiye da 500 bayan kifewar jiragen ruwa a gaɓar Myanmar
Jirgin ruwa na farko yana ɗauke da kusan mutane 250 ya ɓace ba tare da an sake jin duriyarsa ba jim kaɗan bayan ya tashi sannan jirgi na biyu yana ɗauke da kusan mutum 280 wanda ake fargabar ya nutse a a gabar Tekun Ayeyarwady.
Ana fargabar mutuwar 'yan ƙabilar Rohingya fiye da 500 bayan kifewar jiragen ruwa a gaɓar Myanmar
Wani jirgin ruwa, wanda ake zaton yana ɗauke da kusan mutane 250, ya ɓace ba tare da an sake jin duriyarsa ba jim kaɗan bayan ya tashi. / AP

Ana fargabar fiye da mutane 500 sun mutu bayan jiragen ruwa biyu da ke ɗauke da 'yan ƙabilar Rohingya da ake tsangwama a Myanmar sun kife a Tekun Bengal, in ji jami'ai a ranar Alhamis.

A cewar bayanan wucin-gadi da suka fara fitowa, jiragen sun tashi daga jihar Rakhine a yammacin Myanmar a ƙarshen watan Yuni, ɗauke da fasinjoji waɗanda mafi yawa daga cikinsu ‘yan Rohingya ne, ciki har da wasu da suka yi tafiya daga sansanonin 'yan gudun hijira a ƙasar Bangladesh mai maƙwabaka, in ji Hukumar Kula da Hijira ta Duniya (IOM) da Hukumar 'Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (UNHCR) a cikin wata sanarwa ta haɗin gwiwa.

Wani jirgin ruwa, wanda ake zaton yana ɗauke da kusan mutane 250, ya ɓace ba tare da an sake jin duriyarsa ba jim kaɗan bayan ya tashi.

Ana kuma fargabar wani jirgin ruwa na biyu, wanda rahotanni suka ce yana ɗauke da kusan mutane 280, ya nutse a gabar Tekun Ayeyarwady ta ƙasar Myanmar a ranar 8 ga Yuli.

"Ko da yake har yanzu ba a tabbatar da aukuwar lamarin da kuma adadin waɗanda suka mutu a hukumance ba, amma UNHCR da IOM na matuƙar nuna damuwa kan yiwuwar asarar rayuka mai muni da ka iya faruwa," in ji hukumomin.