| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
'Yanbindiga sun kashe mutane 24 a sabbin hare-haren da suka kai a Nijeriya
’Yan bindiga sun kashe mutane 24, ciki har da sojoji takwas da ɗan sanda, a wasu hare-hare guda biyu da suka kai a yankunan arewa maso yamma da tsakiyar Nijeriya a ƙarshen mako, kamar yadda mazauna yankunan da ma’aikatan agaji suka bayyana.
'Yanbindiga sun kashe mutane 24 a sabbin hare-haren da suka kai a Nijeriya
An kashe mutane ashirin da huɗu a wasu hare-hare daban-daban a Najeriya a tsakiyar watan Oktoba na 2026.

’Yan bindiga sun kashe mutane 24, ciki har da sojoji takwas da ɗan sanda, a wasu hare-hare guda biyu da suka kai a yankunan arewa maso yamma da tsakiyar Nijeriya a ƙarshen mako, kamar yadda mazauna yankunan da ma’aikatan agaji suka bayyana ranar Litinin.

A ranar Lahadi, wasu ’yanbindiga sun kashe mutane 13 a wani kwanton-ɓauna da suka yi wa ayarin ’yan kasuwa da ke kan hanyarsu ta zuwa kasuwar yankin a gundumar Bukkuyum, da ke jihar Zamfara a arewa maso yammacin Nijeriya, kamar yadda wasu mazauna yankin uku suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.

Majiyoyin sun ce ayarin, wanda ya taso daga Gwashi, yana kan hanyarsa ta zuwa Gurusu domin halartar kasuwar mako-mako lokacin da ’yan bindigar suka buɗe musu wuta.

Mazauna Bukkuyum uku sun tabbatar da cewa an kashe mutane 13.

“’Yan bindigar sun kashe mutane 13 a kwanton ɓaunan, ciki har da sojoji takwas, ɗan sanda guda ɗaya da ’yan kasuwa huɗu, ciki har da mace,” in ji Lawal Muhammad, wani shugaban al’umma a Bukkuyum.

Ya ce wasu mutane 11, ciki har da sojoji uku, sun ji raunuka kuma an garzaya da su asibiti.

An lalata motoci

Jamilu Umar, wani mazaunin Bukkuyum, ya ce maharan sun wawushe kayayyakin da ke cikin motocin, tare da ƙwace hajojin ’yan kasuwar kafin su ƙona motoci uku da ke cikin ayarin.

A wani hari na daban, wasu da ake zargin ’yan ta’adda ne sun kashe mutane 11 a wani samame da suka kai a gundumar Borgu ta jihar Neja, da ke tsakiyar Nijeriya, kusa da iyakar ƙasar Benin, kamar yadda wasu ma’aikatan agaji biyu suka bayyana.

Dukkansu sun ce an kashe mutane 11 a harin da aka kai cikin daren Asabar zuwa Lahadi.

“’Yanta’addan Lakurawa sun kashe mutane 11, huɗu daga cikinsu kuma ’yan sa-kai ne da ke samar da tsaro ga ƙauyen,” in ji ɗaya daga cikin ma’aikatan agajin.

Ɗayan ma’aikacin agajin ya ce mazauna yankin sun tsere zuwa ƙasar Benin saboda fargabar sake fuskantar wasu hare-hare.