Ziyarar Tinubu a Turkiyya: Muhimman abubuwa a tsarin dangatakar Nijeriya
Ziyarar Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu zuwa Turkiyya tana nuna cikakken ƙoƙarin ƙasashen biyu na ƙarfafa haɗin-gwiwa.
Ziyarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu na Nijeriya zuwa Turkiyya a ranar 26 ga Janairu ta zama alamar wani sabon babi na dangantakar Ankara da Abuja, inda take nuna aniyar ƙasashen biyu ta zurfafa haɗin-gwiwa a harkokin tsaro, diflomasiyya da mu'amalar tattalin arziƙi.
Tattaunawar ta shafi fannoni daban-daban daga tsaro zuwa makamashi, kasuwanci, ilimi da sufurin jiragen sama; ziyarar ta ƙunshi manyan batutuwan tattaunawa na siyasa, da sanya hannu kan yarjejeniyoyi na fahimta a fannoni da dama.
Kafin ziyarar, an ƙara danƙon alaƙar diflomasiyya, inda Ministan Harkokin Wajen Nijeriya, Yusuf Tuggar ya yi tattaunawa da takwaransa na Turkiyya, Hakan Fidan, a ranar Litinin.
Halin kasancewar manyan jami'ai masu alhakin manufofin harkokin waje, tsaro, tsaron cikin gida da leƙen asiri a tawagar Shugaba Tinubu, yana nuna cewa tafiyar ba ta ado ba ce kawai.
Maimakon haka, tana nuna ajanda mai mayar da hankali kan haɗin-gwiwa mai amfani, inda daidaita ayyukan tsaro ya zama ginshiƙi na muradin.
Ziyarar na nuna ƙoƙarin ɗaukaka ingancin dangantakar Turkiyya da Nijeriya a 'yan shekarun baya, zuwa tsarin da ya fi zama kan turbar na ƙungiya kuma mai faɗi. Tana kuma bayyana wannan sauyi a fili a ɓangaren Nijeriya.
AlKasim Abdulkadir, Mataimaki na Musamman kan Kafofin Watsa Labarai da Dabarun Sadarwa ga Ministan Harkokin Wajen Nijeriya, ya ce ziyarar Shugaba Tinubu tana nuna yunƙurin Abuja na faɗaɗa dabarun haɗin-kai fiye da dangantakar dogaro.
Abdulkadir ya shaida wa TRT Afrika cewa, “Ziyarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu zuwa Turkiyya ta zo ne a wani lokaci da Nijeriya ke faɗaɗa abokan hulɗarta fiye da waɗanda take dogaro da su.
Turkiyya ta tsaya a matsayin ƙasa mai masana'antu da matsakaicin ƙarfi, wadda ba ta tare da wani rukunin siyasar duniya.
Ya ƙara da cewa matsayin Turkiyya ya yi daidai da manyan manufofin cigaban Nijeriya na yanzu da kuma na fannin tsaro.
“Ga Nijeriya, Turkiyya na bayar da gamammen haɗin-gwiwa: fannin masana'antu mai ƙarfi daidai da burin gina masana'antunmu, ingantattun ƙwarewar tsaro, da matsayin diflomasiyya mai 'yanci.
A lokacin da Nijeriya ke ba da fifiko ga cigaban masana'antu, gina kayan more rayuwa da daidaita tsaro, Turkiyya ta nuna kanta a matsayin abokiya wanda ke aiwatar da yarjejeniyoyi, daga tsarin mu'amala ta wucin-gadi zuwa haɗin-gwiwa na dogon lokaci,” in ji shi.
Diflomasiyya mai ɓangarori
Turkiyya da Nijeriya sun jima suna samun ra'ayi guda a dandamali mai ɓangarori da yawa kamar D-8 (Kungiyar Haɗin Kan Tattalin Arziki Ƙasashe Musulunci).
Kasancewar Turkiyya mamba a ƙungiyar G20 da ayyukanta na zurfafa diflomasiyya, tare da rawar da Nijeriya ke takawa a ECOWAS da matsayinta a na ƙasa mafi yawan jama'a a Afirka, ya sanya ƙasashen biyu sun zama masu taimakon juna a harkokin duniya.
Ba da ƙarfi da Ankara ke yi kan 'yancin ƙasa da kuma manufarta ta 'cuɗe-ni-in-cuɗe-ka' a hulɗarta da ƙasashen Afirka, tsari ne da zai bai wa Abuja sukunin diflomasiyya mai sassauci, yayin da Nijeriya ke takatsantsan game da tsarin duniya mai dogaro kan Yammacin Turai.
Wannan daidaito yana bayyana a muhawarori kan gyaran tsarin tafiyar duniya. Babban kiran da Shugaba Recep Tayyip Erdoğan ke yi cewa, “duniya ta fi biyar girma”, ya yi daidai da buƙatar Nijeriya ta ƙarfafa wakilcin Afirka a Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, wanda yake ƙarfafa muhimman manufofin da aka gina kan haɗinkan ƙungiyoyi da gyaran tsarin tafiya.
Tsaro da kariya: musaya ƙwarewa
Tsaro yana ci gaba da kasancewa ɗaya daga cikin muhimman fannoni a dangantakar Turkiyya da Nijeriya.
Nijeriya na fama da manyan ƙalubale daga ƙungiyoyin 'yan ta'adda kamar Boko Haram da ISWAP, satar mutane don kuɗin fansa, 'yan fashin daji da ake kira “bandits”, da yawaitar rikice-rikice tsakanin manoma da makiyaya.
“Turkiyya ta haɓaka ƙwarewar tsaro na cikin gida da ƙwarewar yaƙi da ta'addanci da ta dace da barazanar mai fuskoki, wanda hakan ya sanya haɗin-gwiwar tsaro ya zama mai amfani fiye da na maganar baki kawai,” in ji Abdulkadir.
A wannan yanayin, ƙoƙarin Nijeriya na yaƙi da ta'addanci ya haɗu da gogewar Turkiyya ta tsawon shekaru wajen yaƙar ta'addanci da haɓakar masana'antar tsaronta.
Ya ƙara da cewa, “Nasarar Turkiyya wajen gina tsarin masana'antu masu gogayya da masana'antar tsaro zuwa injuna, ya yi daidai da burin masana'antun Nijeriya, inda kamfanonin Turkiyya za su iya samarwa cikin sauri da girma”.
Shigar da helikoftan T-129 ATAK, jirage marasa matuƙa (UAS), da motoci masu sulke sakamako ne na haɗin-gwiwa, wanda har ila yau ya shafi tsaron teku ta hanyar sabunta jirgin rundunar ruwan Nijeriya, NNS ARADU, a Turkiyya.
Ƙwarewar Turkiyya a fannin yaƙi da ta'addanci ana ganin ta a Nijeriya ba kawai a samar da kayan soja ba, har ma a matsayin misali na tsarin ayyuka da na gudanarwa.
Gaza da Somalia: daidaita martanin siyasa
Ankara da Abuja suna nuna kusanci a martani ga manufofin waje da suka ta'allaƙa kan 'yanci, cikakken ikon ƙasa da dokar duniya.
Dangane da mamayar da Isra'ila ta yi na dogon lokaci a yankunan Falasɗinu da yaƙi kisan ƙare dangi a Gaza, Turkiyya da Nijeriya suna yin Allah-wadai da hare-hare kan fararen hula, tilastawar jama’a, da keta dokokin duniya.
Wannan matsayi na haɗinkai ya shafi Somalia, inda duka ƙasashen suka ƙi amincewa da ‘yancin Somaliland a matsayin ƙasa daban, suna gargaɗin cewa hakan zai iya raunana 'yanci da haddasa rashin zaman lafiya a yank Ƙahon Afirka.
Game da irin wannan haɗuwar ra’ayi, Abdulkadir ya ce ƙasashen biyu na kallon rikice-rikice na yankuna da na duniya ta fuskar doka da tsarin haɗin-gwiwa.
“Nijeriya da Turkiyya suna da mahanga iri ɗaya kan tsarin duniya mai girmama 'yanci, cikakken ikon ƙasa da dokar duniya. Wannan tushe na gama-gari yana tsara yadda ƙasashen ke aiki a dandamalin ƙungiyoyi da yawa.
Kan Gaza, duka sun mai da hankali kan kare fararen hula, bada taimakon jin kai da fifita doka ta duniya a kan siyasar iko. Kan Somalia, abin mai da hankali shi ne ƙarfafa ingantattun hukumomin gwamnati, maimakon miƙa 'yanci ga wasu.
Wannan hangen nesa na gama-gari yana ba Nijeriya da Turkiyya damar tsara matsayi tare a ƙasashen duniya cikin sahihanci, ta neman gyara, kaucewa amfani da ƙarfi, da kuma bin doka ba tare da nuna siyasar zalunci,” in ji shi.
Zurfafa tattalin arziƙi da damar zuba jari
Hulɗar tattalin arziƙi ita ce tushe na zahiri a haɗinkan dabaru na Turkiyya da Nijeriya.
Yayin da Abdulkadir yake nuna alfanun kusanci a harkaokin tattalin arziƙi , ya jaddada matsayi na musamman na Turkiyya a kasuwannin duniya da siyasar-da-ƙasa.
“Turkiyya na da tattalin arziki mai haɗa Turai, Gabas ta Tsakiya, Asiya ta Tsakiya da Afirka, kuma wannan matsayi yana da mahimmanci ga 'yan kasuwa da masana'antun Nijeriya.
“A lokaci guda, ikon Turkiyya na mu'amala da duniya yayin da take kiyaye 'yancin manufofi yana da kamanceceniya da burin Nijeriya na samun 'yancin dabaru, haɗin-gwiwa ne ba na sallama kai ba,” in ji shi.
Ko da yake girman cinikayya a yanzu bai kai matakin iya yi ba, ɓangarorin biyu suna ganin burin kasuwanci matsakaici da zai kai dala biliyan biyar a matsayin abin da za a iya samu.
Yayin da kamfanonin Turkiyya ke faɗaɗa kasancewarsu a ɓangarorin kayan more rayuwa, masana'antu da kayayyakin gida a Nijeriya, Nijeriya na ci gaba da kasancewa ƙofa ga Turkiyya zuwa kasuwannin Yammacin Afirka.
Hulɗar kasuwanci tsakanin ƙasashen biyu ta kai dala miliyan $688.4 a cikin watanni goma sha ɗaya na farkon 2025, abin da ke nuna cigaba a yanayi mai hauhawa.
Fiye da kamfanoni 50 na Turkiyya suna aiki a Nijeriya yanzu, tare da jimillar jarin da ake ƙiyasta ya kai kusan dala miliyan $400.
A lokaci guda, kamfanonin kwangila na Turkiyya sun ƙara yawaita a 'yan shekarun nan, inda jimillar darajar ayyukan da aka gudanar a Nijeriya ta kai kusan dala biliyan $3.
Taron kasuwanci da za a yi a ranar Laraba yayin ziyarar zai ƙara nuna ƙoƙarin da ake yi na inganta hulɗar siyasa da haɗinkan tattalin arziƙi mai ƙarfi.
Tare da jimillar cinikayya ta ƙasa da ƙasa ta kusan dala biliyan $2, kuma cinikayyar makamashi na ƙara haɓaka, ana sa ran Nijeriya za ta kasance babbar abokiyar cinikin Turkiyya a Afirka a 2025.
Haɗin-gwiwar makamashi yana ƙara hawa wani muhimmin mataki ga dangantakar tattalin arziƙi. Shigowar LNG daga Nijeriya na taka muhimmiyar rawa a samar da makamashi na Turkiyya, kuma ya dace da babbar manufar Ankara ta faɗaɗa hanyoyin samar da makamashi, wanda ke sanya cinikayyar makamashi ta zama ginshiƙin tattalin arziƙi.
Ilimi da hulɗar al'adu
Ɓangaren ɗan-adam a dangantakar Turkiyya da Najeriya yana ci gaba da zama muhimmin abun da ke tabbatar da haɗin-gwiwa na dogon lokaci.
Da yake nazari kan rawar ilimi da al'adu, Abdulkadir ya yi nuni da ƙwarewarsa da ya samu ta karatu a Turkiyya.
“Bayan karatu a Turkiyya da iya magana da Turkkanci, na ga yadda ilimi da al'adu ke zurfafa diflomasiyya fiye da yarjejeniyar hukuma.
Jami'o'in Turkiyya, cibiyoyin jin-ƙai da al'adu suna ƙirƙirar kyakkyawar alaƙa ta mutane da mutane.
Waɗannan dangantakar mutane na ƙarfafa imanin cewa hulɗar Nijeriya da Turkiyya ba ta zama ta lokaci guda kaɗai ba, har ma ta zama ta dogon lokaci,” in ji shi.
Dangantakar ilimi da al'adu na ci gaba da kasancewa muhimmiya a hulɗar Turkiyya da Nijeriya.
A ƙarƙashin shirin Tallafin Guraben Karatu na Turkiyya, ɗaliban Nijeriya suna samun guraben karatu tun 1992, inda sama da 300 ke karatu a Turkiyya a 2022—wannan ya sanya Nijeriya ta zama tushen ɗaliban Afirka, ta biyu bayan Masar.
Bayan masu samun guraben karatu, fiye da ɗaliban Nijeriya 3,000 sun yi rijista a jami'o'in Turkiyya, ana ganin su a matsayin gada ta gaba tsakanin al'ummomin biyu.
Musayar mutane-da-mutane na samun tallafi ta hanyar jigilar jirage, inda kamfanin Turkish Airlines ke tashi kaitsaye daga Istanbul zuwa Abuja da Legas, ciki har da kusan jirage huɗu a mako a kan hanyar Abuja–Istanbul, wanda ke tabbatar da samun damar zuwa hanyar sufuri ta Turkiyya da duniya.
Hulɗar al'adu na ƙarfafa ta hannun Cibiyar Yunus Emre a Abuja, ta hanyar koyon harshen Turkanci da ayyukan al'adu, yayin da Gidauniyar Turkiyya Diyanet ta samar da ruwansha mai tsabta ga fiye da mutum miliyan ɗaya, ta yi tiyatar ido, shirya tallafin hadaya da ba da guraben ilimi, wanda ya ƙara ƙarfafa ɓangaren jinƙai a dangantaka.
Duban gaba
Ziyarar Shugaba Tinubu zuwa Ankara na wakiltar sabon mataki a dangantakar Turkiyya da Nijeriya. Halartar ministoci masu lura da harkokin waje, tsaro, tsaron cikin gida, kasuwanci da zuba jari ya nuna nufin zurfafa haɗin-gwiwa fiye da hulɗar shugabanni kaɗai.
Dangantakar Turkiyya da Najeriya ta dogara ne kan tarihi mai zurfi, tun daga farkon hulɗa tsakanin Daular Ottoman da daular Kanem-Bornu a ƙarni na 16, zuwa lokacin buɗe Masallacin Shitta-Bey a Legas, da buɗe ofishin jakadancin Turkiyya a 1962.
Ziyarar Tinubu zuwa Ankara tare da babbar tawagar ministoci tana nuna muradin haɓaka wannan gadon tarihin, zuwa haɗin-kai mafi tsari da dabaru don shekaru masu zuwa.