CBN ya bayyana iya abin da mutum zai iya cirewa a ATM duk sati

A ƙarƙashin sabuwar dokar, mutane za su iya cire ₦500,000 ne daga ATM duk mako yayin da kamfanoni za su iya cire naira miliyan biyar.

By
Naira / Reuters

Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya yi shelar sabuwar dokar cire kuɗi da za ta fara aiki ranar 1 ga watan Janairun shekarar 2026, lamarin da zai rage adadin kuɗin da mutane za su iya cirewa daga asusunsu sosai a kowane mako.

A cikin wata sanarwar da aka fitar ranar Talata da sa hannun daraktar manufa da dokokin kuɗi, Dakta Rita I. Sike, CBN ya kawo ƙarshen dokar da a baya ta bai wa ɗaiɗaikun mutane damar cire naira miliyan biyar yayin da ta bai wa kamfanoni damar cire naira miliayan a kowane wata.

A ƙarƙashin sabon umarnin, ɗaiɗaikun mutane iya naira ₦500,000 za su iya cirewa a kowane mako yayin da kamfanoni za su iya cire iya naira miliyan biyar ne kawai.

Duk mai  cire kuɗin da ya zarce wannan zai biya kashi uku cikin ɗari yayin da kamfanonin da suka zarce adadain nasu za su biya kashi 5 cikin 100, kuɗin za a raba tsakanin CBN da bankuna.

CBN ya ce sauye-sauyen sun zama dole domin daidaita manufofin kuɗi na baya da kuma nuna gaskiyar tattalin arziki a yanzu, yana mai lura da cewa tsarin da aka yi wa kwaskwarima yana da nufin rage farashin sarrafa kuɗi, ƙarfafa tsaro, da kuma rage haɗarin halatta kuɗaɗen haram.

An kuma taƙaita yawan kudin da kowane mutum ɗaya zai iya cirewa daga ATM a kullum a matsayin ₦100,000, sai kuma ₦500,000 a duk mako. Bankin ya ƙara da cewa a yanzu ATM za su iya bayar da kowane nau’in kuɗi.