Wata kotu a Afirka ta Kudu ta tuhumi mutane biyu daga cikin mutum uku da ake zargi da satar dalar Amurka 580,000 daga gonar Phala Phala mallakar Shugaban kasar Cyril Ramaphosa, a lardin Limpopo a shekarar 2020, inda ta ce suna da laifi.
Kotun Yankin Modimolle ta samu Imanuwela David da Floriana Joseph da laifin hannu a cikin satar, yayin da wanda ake zargi na uku, Ndilinasho Joseph, aka wanke shi daga dukkan tuhume-tuhumen da ake yi masa.
Alkalin kotun, Peter Manthata, ya bayyana cewa bayanan sadarwa ta wayar hannu sun samar da isassun hujjojin da ke danganta David da Floriana da satar, wadda ta shafi kudaden da ake zargin an boye su a cikin kujerar zama a gonar shugaban kasar.
"Idan aka yi la'akari da dukkan hujjojin da aka gabatar, abin da zan iya fahimta a nan shi ne cewa tattaunawar da ta gudana tsakanin wanda ake zargi na farko da na biyu ta shafi kudaden dalar da aka boye a karkashin kujera a gidan da ke gonar Phala Phala.
Saboda haka, na yanke hukuncin cewa su biyun sun hada baki wajen shiga gidan ba bisa ka'ida ba tare da sace kudaden da ke ciki."
Kamfanin dillancin labarai na gwamnatin kasar, SABC, ya rawaito cewa kotun ta kuma ji cewa David ya yi amfani da wani bangare na kudaden da aka sata wajen sayen mota da kuma gida ga budurwarsa ta wancan lokacin.
Manthata ya ce David ya sayi mata motar Mercedes-Benz C200, wadda darajarta ta kai kimanin rand 500,000, tare da ba ta rand 100,000 a matsayin kudin farko na sayen gida.
Laifin da ba a yada faruwar sa ba
Ba a san da batun satar ba sosai har zuwa watan Yunin 2022, lokacin da Arthur Fraser, tsohon shugaban hukumar leken asiri ta Afirka ta Kudu kuma abokin tsohon shugaban kasar Jacob Zuma, ya bayyana lamarin ga jama'a.
Fraser ya shigar da karar aikata babban laifi kan Ramaphosa, inda ya zargi shugaban kasar da boye batun satar daga 'yan sanda da hukumomin haraji.
Haka kuma ya yi tambayoyi kan yadda shugaban kasar ya tafiyar da lamarin, da kuma yanayin da ya sa aka ajiye makudan kudade na kasashen waje a gonarsa ta kashin kai.
Ramaphosa ya amince cewa an yi satar, amma ya musanta aikata wani laifi.
Bayan zarge-zargen da Fraser ya yi, wani kwamiti mai zaman kansa na majalisar dokoki ya kammala bincikensa a shekarar 2022 da cewa akwai bukatar Ramaphosa ya amsa tambayoyi game da lamarin, wanda hakan ya haifar da yiwuwar fara tsarin tsige shi daga mukaminsa.
Sai dai, 'yan majalisar dokokin sun kada kuri'ar kin amincewa da kafa kwamitin bincike kan tsige shugaban kasar.
A watan Mayun 2026, Kotun Tsarin Mulki ta Afirka ta Kudu ta yanke hukuncin cewa majalisar dokokin ta saba wa doka lokacin da ta kada kuri'ar kin amincewa da rahoton kwamitin ba tare da ta yi nazarin rahoton yadda ya kamata ba.
A watan Yuli, Ramaphosa ya dauki matakin dakatar da binciken majalisar ta hanyar shigar da kara a wata kotun jiha.
Kotun ta dage sauraron karar har zuwa ranar 13 ga watan Nuwamban 2026, domin yanke hukunci.
















