| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Gwamnatin Nijeriya ta ce jihohi 33 da al'ummomi 14,000 na cikin hadarin ambaliyar ruwa a 2026
Haka nan, akwai wasu ƙarin ƙananan hukumomi 77 da ake hasashen za su fuskanci haɗarin ƙaramar ambaliya a al’ummomi 923 cikin ƙananan hukumomi 77 a jihohi 24.
Gwamnatin Nijeriya ta ce jihohi 33 da al'ummomi 14,000 na cikin hadarin ambaliyar ruwa a 2026
Ambaliyar ruwa tana shafar garuruwan Nijeriya duk lokacin damina. / Reuters
6 awanni baya

Yayin da lokacin damina ke kankama a yawancin yankunan Nijeriya, gwamnatin ƙasar ta yi gargaɗi kan barazanar ambaliyar ruwa da ke fuskantar yankuna da alu’ummomin cikin ƙasar.

A ta bakin Ministan Albarkatun Ruwa da Tsabtar Muhalli na Nijeriya, Joseph Utsev, a 2026 jihohi 33 da kuma al'ummomi dubu sha huɗu da ɗari ɗaya da goma sha takwas suna cikin haɗarin ambaliyar ruwa.

Ministan ya sanar da haka ne a Abuja ranar Laraba, yayin taron gabatar da hasashen ambaliyar ruwa na shekara-shekara da hukumar ayyukan ruwa ta ƙasar ta yi.

Yawan al’ummomin da ke cikin babban haɗarin fuskantar ambaliya suna a ƙananan hukumomi 266 da ke cikin johohi 33, da kuma babban birnin tarayyar ƙasar, FCT.

Jihohin sun haɗa da Abia, Adamawa, Anambra, Bauchi, Bayelsa, Benue, Borno, Cross River, Delta, Ebonyi, Edo, Enugu, Gombe, Imo, Jigawa, Kaduna, Kano, Kebbi, Kogi, Kwara, Lagos, Nasarawa, Niger, Ogun, Ondo, Osun, Oyo, Plateau, Rivers, Sokoto, Taraba, Yobe, Zamfara, da kuma FCT.

Sai dai baya ga waɗannan, akwai ƙarin ƙananan hukumomi 405 a jihohi 35 da ke cikin tsaktsakin haɗarin ambaliyar, idan ban da jihar Ekiti.

Haka nan, akwai wasu ƙarin ƙananan hukumomi 77 da ake hasashen za su fuskanci haɗarin ƙaramar ambaliya a al’ummomi 923 cikin ƙananan hukumomi 77 a jihohi 24.

Sabon tsarin da aka bayyana a bana, ya nuna hasashen ambaliya a matakin al’ummomi, maimakon ƙananan hukumomi da johohi kawai.

Bayan gabatar da hasashen ambaliyar, wakilin shugaban Nijeriya a taron, Ministan Muhalli, Balarabe Lawal, ya nanata ƙudurin shugaba Bola Tinubu kan ƙarfafa tsare-tsaren kai ɗauki a faɗin ƙasar yayin ambaliya.