| Hausa
GABAS TA TSAKIYA
2 minti karatu
Vance zai tafi Pakistan ranar Talata domin tattaunawa da Iran — rahoto
Fadar White House tana jiran bayyananniyar alama ne daga Tehran kan ko za ta amince ta tura tawagarta ta tattaunawa zuwa Islamabad domin zagaye na gaba na tattaunawa, in ji Axios.
Vance zai tafi Pakistan ranar Talata domin tattaunawa da Iran  — rahoto
Mataimakin shugaban ƙasan Amurka JD Vance zai jagoranci wata tawaga zuwa Pakistan domin tattaunawar sulhu da Iran. (TSOHON HOTO) / Reuters

Mataimakin shugabna Amurka JD Vance zai tafi Pakistan ranar Talata domin tattaunawa kan Iran, in ji kafofin watsa labaran Amurka.

Ana sa rai Vance zai tafi Islamabad da safiyar Talata domin tattaunawa da Iran kan yiwuwar yarjejeniya ta kawo ƙarshen yaƙin, kamar yadda kafar watsa labaran Amurka Axios ta ruwaito ranar Litinin, inda ta ambato majiyoyin Amurka uku.

Fadar White House ta shafe ranar Litinin tana jiran wata alama daga Tehran kan cewa za ta tura tawagarta zuwa Islamabad, in ji rahoton.

Masu shiga tsakani sun nemi jami’an Iran su halarci tattaunawar, suna masu kira a gare su su tura wata tawaga.

Tehran ba ta yi sanar da yanke hukuncin tura wata tawaga ba tukunna.

Sai dai kuma, majiyoyin Pakistan sun shaida wa New York Post cewa Tehran na "son tura [tawaga] zuwa zagaye na biyu," amma cewa "ba a yanke hukunci ba tukunna game da batun”.

Inda hankali zai karkata

Steve Witkoff da Jared Kushner da sauran manyan jami’ai na da yiwuwar kasancewa a tattaunawar, amma Vance ne hankali zai karkata akansa, in ji jaridar The New York Times.

An bai wa mataimakin shugaban Amurka aikin samar da hanyar da Amurka za ta fice daga yaƙin da mutane da dama ke ƙin jini a Amurka kuma yake ci gaba da matsi kan tattalin arzikin duniya da kuma hanyar samar da makamashinsa mai sarƙaƙiya.

Wannan nauyin na diflomasiyya na zuwa ne ya yi da aka riga aka fara ƙoƙarin sake buɗe hanyar tattaunawa da Tehran, duk da cewa ƙoƙarin na samun taƙaitacciyar nasara.

Pakistan ta karɓi baƙuncin tattaunawa kai-tsaye ta farko tsakanin manyan jami’an Amurka da na Iran daga ranar 11 zuwa 12 ga watan Afrilu, ganawa ta manyan jami’ai ta farko tun lokacin da ƙasashen biyu suka yanke hulɗar diflomasiyya a shekarar 1979, amma wannan tattaunawar ta ƙare ne ba tare da mafita ba.

An saka Islamabad cikin wani aynayi na tsattsaurar tsaro ranar Lahadi da dare inda hukumomi suka tabbatar da baza ƙarin ‘yansanda a faɗin birnin.