Dalilai uku na ɗage shari'ar tabbatar da Sarkin Kano a Kotun Ƙolin Nijeriya

Wasu dalilai sun tilasta wa kotun ƙolin Nijeriya ɗage shari'ar da aka kai gwamnatin Kano da ke arewacin ƙasar, kan naɗin sarkin Kano.

By
Yanzu sai zuwa Afrilun 2026 za a ci gaba da shari'ar. / Reuters

Masana shari’a a Nijeriya sun yi sharhi kan ɗage shari’ar tantance waye Sarkin Kano da ke Jihar Kanon Nijeriya, bayan da Kotun Ƙolin ƙasar ta fasa yin zaman ci gaba da shari’ar sai nan da shekara guda.

A ranar Litinin, 20 ga Afrilun 2026 ne Kotun Ƙolin Nijeriya ta ce ta ɗage batun ƙarar sai zuwa ranar 17 ga Afrilun 2027, kamar yadda alƙalin kotun, Mai Shari’a Adamu Jauro ya ambata.

Lauyoyi da masu sharhi kan batun sun bayyana dalilan da suka janyo wannan ɗagewar.

Na farko, lauyoyin masu kare kansu a shari’an sun gabatar da wani ƙuduri tun a ranar 14 ga Afrilun 2026, inda aka ce takardar ba ta kai ga ɗaya ɓangaren ba sai ranar 15 ga Afrilun.

Na biyu, bisa doka, ana bai wa lauyoyin da aka gabatar wa ƙuduri tsawon mako biyu don su mayar da raddi. Don haka dole a ba su wannan haƙƙi kafin ci gaba da shari’ar.

Na uku, kasancewar gabatar da ƙudurin zai kawo jinkirin idan aka zo zaman kotu a yau, Kotun Ƙolin ta zaɓi da jingine sauraron ƙarar kacokan, sai nan da shekara guda.

Da yake sharhi kan dalilin saka tsawon shekara guda kafin ci gaba da ƙarar, lauya cikin lauyoyin masu ɗaukaka ƙara, Barrister Mamman Lawan Yusufari ya ce, saɓanin yadda wasu ke ambatawa, zaman na yau saurare aka shirya yi ba yanke hukunci ba.

A wata hira da kafar yaɗa labarai ta DCL Hausa, Yusufari ya ce wannan ba baƙon abu ba ne, ganin cewa Kotun Ƙolin na da tarin shari’u da ke gabanta, kuma shekara guda ɗin ma bai yi nisa ba a yadda kotun ta saba aikinta.

Tarihin shari’ar

A watan Mayun 2024 ne gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya sauya dokar naɗa sarakuna a jihar, sannan ya sake nada Malam Muhammad Sanusi II a matsayin Sarkin Kano na 16, tare da sauke Sarki na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero.

Da ma dai gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ce ta sauke Malam Muhammadu Sanusi II daga zama Sarkin Kano ranar 9 ga Maris ɗin 2020.

Wanda ya ɗaukaka ƙara zuwa gaban Kotun Ƙoli ta yanzu shi ne Alhaji Aminu Babba Dan Agundi, wani hakimi a fadar Sarki Aminu Bayero, bayan da ya ƙi amincewa da hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara na Janairun 2025.

A yanzu dai masu ruwa-da-tsaki a shari’ar kan waye sahihin Sarkin Kano, za su jira zuwa lokacin da Kotun Ƙolin za ta sake waiwayar wannan batu.