Hukumar ƙwallon ƙafar Sifaniya ta maye gurbin Lamine Yamal da Jorge de Frutos
Hukumar ƙwallon ƙafa ta Sifaniya (RFEF) ce ta tabbatar da wannan labarin a wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X ranar Talata.
Kocin tawagar ƙwallon ƙafa ta Sifaniya, Luis de la Fuente ya ɗauki wani mataki na gaggawa na gayyatar Jorge de Frutos domin maye gurbin Lamine Yamal wanda bai je sansanin horarwar tawagar ba bisa dalilai na jinya.
Hukumar ƙwallon ƙafa ta Sifaniya (RFEF) ce ta tabbatar da wannan labarin a wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X ranar Talata.
Lamine Yamal da ke taka leda a ƙungiyar Barceola ana masa kallon mahimmin ɗan wasa a tawagar ƙwallon ƙafar Sifaniyar. Sai dai kuma ya bar sansanin wasan ne sakamakon rashin jin daɗi lamarin da ya hana shi wajen atisaye yadda ya kamata.
De Frutos, wanda aka sani da iya gudunsa da kuma ikon iya cin galaba a kan masu tsaron gida a gefe, zai shiga cikin ‘yan wasan tawagar nan take.
Wannan gayyatar wata babbar matsaya ce a tarihin taka ledar Jorge de Frutos.
Jajircewarsa wajen dabarar murza leda da kuma taimakon da yake bayarwa wajen zura ƙwallo a raga sun taka rawar gani wajen samar masa wannan sakamakon.
Tawagar ƙwallon ƙafar Sifaniyar dai za ta kara da tawagwar ƙwallon ƙafar Georgia da Turkiyya a ƙarshen wannan makon a wasannin neman shiga Gasar Cin Kofin Duniya a ƙarshen mako da kuma ranar Talata mai zuwa.