KGasar FIFA 2026 za ta sha bamban da sauran gasannin Kofin Duniya da aka yi a baya. A bana za a buga gasar ne a ƙasashen Amurka, Canada, da Mexico, daga ranar Alhamis 11 ga Yuni, zuwa Lahadi, 19 ga Yulin 2026.
Kofin Duniya shi ne kambin wasanni da aka fi son ɗagawa a duniya, kuma ɗaya daga cikin mafi daraja a kayayyakin alatu na wasanni a faɗin duniya.
Idan aka duba zunzurutun zinaren da aka yi kofin da shi, wato karat 18, a farashin yanzu ya kai dala $250,000. Amma da za a yi gwanjon sa a kasuwar duniya, to sai ya kai aƙalla dala miliyan $20.
Shuhurar Gasar Kofin Duniya ta samo asali ne saboda ita ce gasa mafi girma, mafi tsada, kuma mafi armashi, shagali, da sharholiya, wadda ke jan hankalin duniya ba wai a ɓangaren wasanni ba, har a fannin tallata hajar manyan kamfanoni.
Ga muhimman bayanai biyar game da gasar ta bana:
Yawan ƙasashe
Bayan rairaye ƙasashen duniya ta hanyar buga wasannin neman cancanta, a yanzu jimillar ƙasashe 48 ne za su fafata a gasar. Wannan ne karo na farko da ƙasashe 48 za su buga gasar, inda kafin yanzu, ƙasashe 32 ne kacal suke buga ta.
An raba ƙasashen 48 zuwa rukunoni 12, kuma dangane da wakilcin nahiyoyin, Turai na da rinjaye da ƙasashe 16, sai Afirka mai ƙasashe 10, sai ƙasashe 9 daga Asiya, sai ƙasashe 6 daga nahiyar Amurka ta Kudu, da ƙasashe 6 daga Amurka ta Arewa, sai kuma ƙasa 1 daga nahiyar Oceania.
A bana, ƙasashe 4 ne za su buga gasar a karon farko a tarihinsu, wato ƙasashen Jordan, Cape Verde, Curacao, da Uzbekistan.
Wuraren wasanni
Rabon da a buga gasar Kofin Duniya a nahiyar Amurka tun a 1994, lokacin da aka buga ta a ƙasar Amurka, wato shekaru 32 da suka gabata kenan. Sai dai a wannan karon, a ƙasashe uku za a buga ta, wato Amurka, Canada, da Mexico.
Duka wasannin za su gudana a birane 16 na ƙasashen uku, wato birane 11 a Amurka, birane uku a Mexico, sai kuma birane biyu a Canada.
Jimillar wasanni
A gasar ta bana za a buga wasanni mafi yawan da aka gani a tarihin gasar, inda za a buga jimillar wasanni har 104.
Yawancin wasannin za su gudana ne a Amurka, amma a Mexico za a buɗe gasar da wasa tsakanin Mexico da Afirka ta Kudu, sannan a yi bikin rufewa a filin wasa na MetLife da ke jihar New Jersey ta Amurka.
Yawan kudi
FIFA za ta biya jimillar zunzurutun kuɗi dala miliyan $665 ga ƙasashe 48 da ke halartar gasar. Duk ƙasar da ta ɗaga kofin za ta samu tsabar kuɗi dala miliyan $50.
Ƙasa ta 2 za ta samu dala miliyan $33, ta 3, dala miliyan $29, ta 4, dala miliyan $27, ta 5 zuwa ta 8, dala miliyan $19. Sai ta 9 zuwa ta 16, dala miliyan $15, ta 17 zuwa ta 32, dala miliyan $11, sannan ta 33 zuwa ta 48, dala miliyan $9.
Bugu da ƙari, akwai dala miliyan $1.5 ga kowace ƙasa a matsayin kuɗin shirye-shirye. Wato dai, duk ƙasar da ta je gasar za ta tsira da aƙalla dala miliyan $10.5, ko da an fitar da ita a matakin rukuni, ko da kuwa ba ta ci ko da wasa guda ba.
Tikitin wasanni
Ga masu son kallon wasannin ido-da-ido, ana sayar da tikitin wasannin matakin rukunin kan mabambantan farashi, inda mafi arahar tikiti, kamar na wasan Ivory Coast da Curacao, wanda ba a samu masu neman sa da yawa ba, yake kai wa dala $400.
Sai tikiti mai tsananin tsada saboda yawan masu buƙatar sayan sa, kamar na wasan ranar buɗewa, tsakanin Mexico da Afirka ta Kudu, wanda yake kai wa har dala $4,000.
Farashin tikitin wasannin ƙarshe yana hauhawa, inda yakan kama daga dala $5,785, har zuwa dala $10,990.
Sannan akwai tikiti na matakin gangariya, wato “Premium Category 1”, wanda ake samun wajen zama a gaba-gaba, dab da ‘yanwasa. Kuma farashinsa yakan kai zunzurutun kuɗi har dala $33,000.












