| Hausa
WASANNI
2 minti karatu
An dakatar da mai tsaron ragar FC Andorra wasanni 12 bisa zama sanadin mutuwar Jesus de Miguel
Lamarin ya faru ne yayin wasan rukuni na biyu na gasar ƙwallon ƙafa ta Sifaniya a ranar 2 ga Nuwamba, lokacin da Owono ya fito daga cikin raga zuwa tsakiyar fili domin ƙoƙarin ƙwace wata ƙwallo da aka bugo sama, inda suka yi karo da Miguel.
An dakatar da mai tsaron ragar FC Andorra wasanni 12 bisa zama sanadin mutuwar Jesus de Miguel
Alƙalin wasa ya bai wa mai tsaron ragar jan kati bayan wannan arangama / AP (Wire)

An dakatar da mai tsaron ragar ƙungiyar FC Andorra, Jesus Owono har wasanni 12 sakamakon arangamar da ta yi sanadin mutuwar ɗan wasan gaban ƙungiyar Tenerife, Jesus de Miguel.

Kwamitin ladabtarwa na hukumar ƙwallon ƙafa ta ƙasar Sifaniya ce ta dakatar da Owono.

Lamarin ya faru ne yayin wasan rukuni na biyu na gasar ƙwallon ƙafa ta Sifaniya a ranar 2 ga Nuwamba, lokacin da Owono ya fito daga cikin raga zuwa tsakiyar fili domin ƙoƙarin ƙwace wata ƙwallo da aka bugo sama, inda suka yi karo da Miguel.

Alƙalin wasa ya bai wa mai tsaron ragar jan kati bayan wannan arangama. De Miguel mai shekaru 30 ya gamu da bugun zuciya, inda aka garzaya da shi asibiti, amma ya rasu washegari.

Kwamitin ladabtarwa ya ɗauki matakin hukunci mafi tsauri

A hukuncin da ya yanke ranar Juma’a, kwamitin ya ce rahoton alƙalin wasan ya nuna cewa an kori Owono daga fili ne saboda “bugun abokin hamayyarsa a ƙirji da ƙafarsa ƙarfi mai tsananin, ba tare da la'akari da iyakar ƙarfin da ya kamata a yi amfani da shi ba, a lokacin da ake ci gaba da wasa”.

Kwamitin ya ce ya yi la'akari da mummunan sakamakon da lamarin ya haifar, inda ya bayyana cewa yanayin abin da ya faru da kuma abubuwan da suka dabaibaye shi sun sa ya dace a ɗauki matakin hukunci mafi tsauri na dakatar da shi na wasanni 12.

Owono ya bayyana alhinin mutuwar De Miguel

Owono, wanda ke wakiltar ƙasar Equatorial Guinea a matakin ƙasa da ƙasa, ya bayyana kwanakin da suka biyo bayan mutuwar De Miguel a matsayin “mafi wahalar kwanaki a rayuwarsa”.

Owono a cikin wata sanarwa da ƙungiyarsa ta fitar a makon da ya gabata ya ce: “Na rasa kalmomin da zan bayyana abin da ke zuciyata, kuma yana da matuƙar wahala a gare ni in fahimci duk abin da ya faru.”

Ya ƙara da cewa: “Ina cikin matuƙar baƙin ciki sakamakon rasuwar Jesus. Ina tunaninsa, da iyalansa, da kuma dukkan mutanen da suke ƙaunarsa.”