Dalilai huɗu da suka sa matasan Afirka suka fi lafiyar ƙwaƙwalwa a duniya

Matasan Ghana ne suka ciri tuta saboda su ne suka zo na daya yayin da matasan Nijeriya suke biye a mataki na biyu a lafiyar ƙwaƙwalwa kamar yadda rahoton ya bayyana.

By
Matasan Afirka

Wani sabon bincike da aka yi a duniya da aka yi wa lakabi da 2025 Global Mind Project ya bayyana cewa kasashen Ghana, Nijeriya, Kenya, Zimbabwe, da kuma Tanzania su ne kan gaba a jerin kasashen da matasansu suka fi lafiyar ƙwaƙwalwa.

Yayin da kashi 41 cikin 100 na matasan duniya ke fama da damuwa da matsalolin ƙwaƙwalwa, matasa a kasashe kamar Ghana da Nijeriya su ne kan gaba a lafiyar ƙwaƙwalwa, kamar yadda cibiyar nazari kan tunanin ɗan’adam ta Sapien Labs ta bayyana.

Binciken ya yi amfani da ma’aunin Mind Health Quotient (MHQ) don auna bangarori 47 na rayuwa kuma ya yi nazari ne kan matasa wadanda suke tsakanin shekara 18 zuwa 34 a kasashen duniya daban-daban.

Matasan Ghana ne suka ciri tuta saboda su ne suka zo na daya yayin da matasan Nijeriya suke biye a mataki na biyu a lafiyar ƙwaƙwalwa kamar yadda rahoton ya bayyana.

Matasan Kenya su ne na mataki na uku, sai na Zimbabwe a matsayi na hudu yayin da matasan Tanzania suke matsayi na biyar.

Galibi kasashen  yammancin duniya kamar Amurka da Birtaniya da Kanada suna ƙasa-ƙasa ne a jerin, kamar yadda rahoton ya bayyana.

Ga manyan dalilai hudu da suka sa aka samu wannan nasara a wadannan kasashen Afirka biyar a cewar rahoton:

Na farko Wayar Hannu: Yara ba sa saurin mallakar wayar kansu sai sun ɗan girma a kasashen Afirka. Binciken ya nuna cewa samun waya da wuri yana lalata tunanin yara da jefa su cikin damuwa.

Sai dalili na biyu wato bambancin cimaka ko kuma na ce abinci.  Kasashen Afirka ba su cika cin abincin gwangwani ko wanda aka sarrafa sosai a masana’antu ba kamar yadda ake ci a kasashen Turai da Amurka.

Abu na uku shi ne kusanci da iyali wato: Duk da cewa abubuwa na sauyawa, har yanzu akwai danƙon zumunci a tsakanin iyalai da ’yan’uwa da abokan arziki a kasashen Afirka fiye da yadda mutanen da ke Turai da Amurka suke alaka da kuma hulda da junansu.

Abu na hudu da rahoton ya alakanta nasarar da kasashen Afirka suka samu da shi, shi ne addini ko aƙida. Kasar Tanzania ce ta daya a duniya wajen riƙo da addini a cewar rahoton, kuma binciken ya ce duk wanda ya yi riƙo da addini kowane iri ne, to hakan yana kare mutum daga faduwar gaba da yanke ƙauna kan rayuwa.

Ko da yake wannan babbar nasara ce ga kasashen Afirka, masana sun yi gargaɗi cewa duk da cewa galibin kasashen Afirka na gaban kasashen Turai da Amurka, amma rahoton ya ce lafiyar ƙwaƙwalwar matasanmu tana raguwa idan aka kwatanta da ta iyayenmu.

Shugabar binciken, Tara Thiagarajan ta ce wannan matsala tana shafar yadda matasa a ko ina suke sarrafa fushi (Emotional Control), da yadda suke mu’amala da mutane (Relationship), da kuma mayar da hankali kan ayyukansu (Focus).

Masanan sun yi gargadi cewa idan matasan kasashen Afirka ba su yi hankali ba, fasahar zamani da abincin zamani za su iya ruguza wannan nasara.

Mece ce mafita? Masana sun ba da shawarar taƙaita amfani da waya ga yara, da rage cin abincin da aka sarrafa a masana’antu da komawa cin abincin gida, da kuma ƙarfafa danƙon zumunci a tsakanin jama’a da duƙufa wajen tarbiyyar iyali.