Tururin nukiliya zai jawo asarar rayuka a manyan biranen ƙasashen Gulf ba Tehran ba: Araghchi
"Isra’ila da Amurka sun jefa bam tashar Bushehr sau huɗu yanzu. Fitar tururin zai kawo asarar rayuka a manyan biranen ƙasashen GCC, ba a Tehran ba,"in ji Abbas Araghchi a rubutun da ya yi a shafinsa na X a ranar Asabar.
Ministan Harkokin Wajen Iran ya ce "fitar tururin makamashin nukiliya zai kawo ƙarshen rayuka a manyan biranen ƙasashen Gulf ba Tehran ba,” bayan Isra’ila ta kai hari tashar makamashin nukiliya ta Iran ta Bushehr.
“Kun tuna fushin ƙasashen Yamma game da rikice-rikice a kusa da Tashar Makamashin Nukiliya ta Zaporizhzhia a Ukraine?
"Isra’ila da Amurka sun jefa bam tashar Bushehr sau huɗu yanzu. Fitar tururin zai kawo asarar rayuka a manyan biranen ƙasashen GCC, ba a Tehran ba,"in ji Abbas Araghchi a rubutun da ya yi a shafinsa na X a ranar Asabar.
Araghchi ya ce hare-haren kan matatun sinadarai na Iran sun kuma bayyana "ainihin manufofin."
A baya a ranar, hare-haren Amurka da Isra'ila sun sauka kan tashar makamashin nukiliya ta Bushehr a Iran, inda suka kashe mutum ɗaya.
Harin ya zo yayin da tashin hankali a yankin ya ƙaru tun bayan da Amurka da Isra'ila suka ƙaddamar da wani farmaki na haɗin gwiwa kan Iran a ranar 28 ga Fabrairu, wanda ya kashe mutane fiye da 1,340 zuwa yanzu, ciki har da a tsohon jagoran adddini na ƙasar Ali Khamenei.
Tehran ta mayar da martani da harin jiragen sama marasa matuƙa da makamai masu linzami a kan Isra'ila da Jordan da Iraki da ƙasashen Gulf waɗanda suka ba sojojin Amurka masauki.