Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta nahiyar Turai (UEFA) da ta Asia (AFC) da ta Arewaci da Tsakiyar Amurka da kuma yankin Caribbean (CONCACAF) a ranar Litinin sun zargi Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Duniya (FIFA) da wani “gagarumin cin amana” game da yadda take tafiyar da batun niyyar sayar da wani ɓangare na haƙƙin talla na Gasar Kofin Duniya.
A wata sanarwa ta haɗin gwiwa, hukumomin ƙwallon ƙafa na nahiyoyin uku sun ce rashin jituwar batu ne na “ingancin wasa” kuma sun yi kira ga shugaban FIFA da a ringa fayyace gaskiyar komai a fili.
“Wasan ƙwallon ƙafa shi ne abu mafi ƙarfi da mutane da yawa suka fi ƙauna. Ba na wani mutum ɗaya ko wata hukuma ɗaya ba ne,” in ji su, suna masu ƙarawa da cewa wasan na ‘yanwasa ne, da magoya baya, da ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa, da hukumomin ƙwallon ƙafan da aka bai wa amanar ƙare makomarsa.
Sanarwar ta ce wasiƙar FIFA ta kwanan nan zuwa mataimakan shugaban hukumar da kuma hukumomin ƙwallon ƙafa na ƙasashe 211 ta yarda da cewa akwai kurakurai a cikin tsarin, amma ta bayyana su a matsayin matsala ta ƙatsewar sadarwa.
Hukumomin ƙwallon ƙafar nahiyoyin sun ce batun ya ɗara matsalar tarnaƙin sadarwa, suna masu cewa an gabatar da shawarwarin ne cikin wani tsukakken jadawali ba tare da wata tuntuɓa mai ma’ana ba, tare da wani wa’adi da ya taƙaita damar hukumomin ƙwallon ƙafa, mambobin hukumar na nazari kan tanade-tanaden yadda ya dace.
Sun kuma ce FIFA ta gaza yarda da cewa shawarar da kanta tana da muhimmiyar tawaya, suna masu bayyana ƙoƙarin sayar da wani ɓangare na hannayen jarin Gasar kofin Duniya a matsayin wani babban kuskure mai muni da kuma cin amanar hukumomin da ya kamata a ce FIFA na yi wa hidima.
Kira ga nazari na wata tawaga daga waje
Hukumomin ƙwallon ƙafar na nahiyoyin sun yi kira da a samu wata kafa mai cin gashin kanta da za ta iya nazari kan batun, suna masu cewa kada FIFA ta yi binciken da kanta ko kuma ta hanyar ma’aikatanta ko kuma wasu masu ruwa da tsaki na ƙwallon ƙafa.
Sun kuma yi kira ga kare dukkan takardun da ke da alaƙa da batun tare da bayanai.
Sanarwar ta nuna ƙarin damuwa game da zaman shugabancin na kwanan nan a Maroko, tana mai cewa bayanan FIFA na kanta sun nuna cewa zaɓaɓɓen jami’i ɗaya ne kawai ya halarci taron, kuma babu wani mamban kwamitin zartarwar FIFA ko kuma hukumomin ƙwallon ƙafa na ƙasashen da aka gayyata .
Maimakon haka, manyan jami’an FIFA da ke aiki a kwamitin gudanarwa ne suka halarci zaman.
Hukumomin ƙwallon ƙafar na nahiyoyin sun ce matakin kiran wani ɓangare na kwamitin gudanarwa zuwa ƙetare, maimakon saka shugabancin FIFA ya yi bayani game da lamarin a hedikwatarta a Zurich ya ƙara ƙarfafa damuwarsu game da salon yadda ake tafiyar da hukumar.
Sun kuma ce lamarin ya nuna wani salon ɗabi’a da bai dace da aikin FIFA a matsayin mai tafiyar da lamuran ƙwallon ƙafa ba.
“Ana shiru inda ya kamata a fayyace gaskiya, ana nesa a inda ya kamata a buɗe ƙofa. Waɗannan ba ɗabi’un da suka dace da shugabancin ƙwallon ƙafa ba ne,” in ji su.
Sanarwar ta zo ne bayan UEFA ta sake jaddada cewa za ta ci gaba da ƙaurace wa dukkan gasar FIFA, duk da cewa Shugaban FIFA Gianni Infantino ya janye shawarar kuma ya nemi gafara kan yadda aka tafiyar da lamarin. FIFA ta yi watsi da shirin bayan ya haifar da adawa mai tsanani daga hukumomin ƙwallon ƙafa.
UEFA ta bayyana a baya cewa hukumomin ƙwallon ƙafa mambobinta za su ƙaurace wa duk gasar FIFA idan aka ci gaba da shawarar.




















