| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Fiye da mutum 1,000 ne suka tsere wa hare-haren 'yanbindiga a jihar Benue ta Nijeriya
Maharan sun afka wa al'ummar Ankpechi da ke gundumar Oglewu ta karamar hukumar Ohimini a safiyar Alhamis, inda suka tilasta wa mazauna yankin barin gidajensu su nemi mafaka a al'ummomin da ke makwabtaka, a cewar jami'an yankin.
Fiye da mutum 1,000 ne suka tsere wa hare-haren 'yanbindiga a jihar Benue ta Nijeriya
Benue, na daya daga cikin manyan jihohin da ake noma a Nijeriya, ta fuskanci rikice-rikice da ke da alaka da kungiyoyi masu dauke da makamai

Fiye da mutum 1,000 ne suka tsere daga gidajensu bayan da wasu da ake zargin ‘yan fashi da makami ne suka kai hari ga al’ummar Ankpechi da ke jihar Benue a yankin arewa maso tsakiyar Nijeriya, kamar yadda mazauna yankin suka bayyana a ranar Alhamis, a daidai lokacin da wani sabon tashin hankali ya afka wa yankin da ke samar da abinci a Nijeriya.

Maharan sun afka wa al'ummar Ankpechi da ke gundumar Oglewu ta Ƙaramar Hukumar Ohimini a safiyar Alhamis, inda suka tilasta wa mazauna yankin barin gidajensu su nemi mafaka a al'ummomin da ke makwabtaka, a cewar jami'an yankin.

Garin yana a hanyar Otukpo–Ogobia sannan tana kusa da Ondo-Ugboju a Karamar Hukumar Otukpo, inda a kwana nan 'yan bindiga suka kona wasu gidaje.

Kazalika, Shugaban Karamar Hukumar Ohimini, Gabriel Adole, ya tabbatar da harin.

Neman mafaka a al'ummomin da ke kusa

"Mahara sun mamaye al'ummar a safiyar Alhamis," kamar yadda Adole ya shaida wa manema labarai a Makurdi, babban birnin jihar ta Benue.

Ya ce an kori mazauna yankin daga gidajensu sakamakon harin kuma suna neman mafaka a al'ummomin da ke kusa, yayin da aka tura jami'an tsaro zuwa yankin don dakile sake aukuwar hare-haren.

Harin na baya-bayan nan ya zo ne kwanaki kaɗan bayan wasu munanan hare-hare da aka kai yankin karamar hukumar Otukpo da ke makwabtaka da jihar, lamarin da ke nuna karuwar rashin tsaro a sassan jihar Benue, inda kungiyoyi masu dauke da makamai suke yawan kai hari kan kauyuka, sannan suna kashe mazauna, tare da lalata gidaje, da kuma tilasta wa dubban mutane tserewa.

Benue, na ɗaya daga cikin manyan jihohin da ake yin noma a Nijeriya, kuma ta fuskanci rikice-rikice da ke da alaƙa da ƙungiyoyi masu dauke da makamai da kuma takaddamar da ta dade tana faruwa kan gonaki da dabbobin da ake kiwo.

Hare-haren da ake yawan kai wa sun raba dubban mutane da muhallinsu, sannan sun janyo cikas ga ayyukan noma da kara dagula yanayin ayyukan jinƙai a faɗin jihar.

Rumbun Labarai
WAEC ta riƙe sakamakon jarrabawar ɗalibai 167,486
Dakarun Nijeriya sun kama mutanen da ake zargi da kai wa  'yan Boko Haram ƙwayoyi a Borno da Yobe
Gwamnati ta ba jami’o’i da kwalejojin Nijeriya umarnin korar ɗalibai da ke da alaka da satar mutane
'Yansandan Nijeriya sun kama mutum 48 a samamen da suka kai maɓoyar masu laifi a Zamfara
An saki alƙalin da aka yi garkuwa da shi a jihar Kebbin Nijeriya
Dakarun Nijeriya sun daƙile harin daren 'yanta'adda kan sansanin soji
'Yanbindiga sun kashe mutum 12, sun yi garkuwa da mata da yara a wani ƙauye Sokoto a Nijeriya
Nijeriya ta tura sojoji 86 domin aikin wanzar da zaman lafiya a Guinea-Bissau
Sojojin Nijeriya sun daƙile yunƙurin 'yanta'adda na garkuwa  da mutane 31 a Borno
Remi Tinubu ta nemi Saudiyya ta tallafa wa ilimin almajirai a Nijeriya
Nijeriya ta lalata makamai guda 2,819 da ta kama a matakin dakile rashin tsaro
'Yansandan InterPol sun tasa ƙeyar ɗan China daga Nijeriya kan safarar namun daji
Nijeriya na da attajirai 7,200 masu arzikin dala miliyan 1 duk da raguwar kuɗi - Rahoto
'Yanbindiga sun kashe Kanar na sojin Nijeriya bayan ya ƙi amincewa su yi garkuwa da shi
Aƙalla mutane 14 ne suka mutu a wani hari da aka kai a jihar Benue ta Nijeriya, in ji jami’an yankin
'Yanta'adda sun kashe aƙalla mutum 30 a wani ƙauye a Kaduna ta Nijeriya
Ana fargabar ɗalibai sun maƙale bayan da gini mai ɗakuna 90 ya rufta da su
Rundunar Sojin Nijeriya ta kama jami'in da ake zargi da sayar wa 'yanta'adda kayan soji
Jami'in da ke kula da harkokin kuɗin ISWAP ya miƙa wuya —Rundunar Sojin Nijeriya
INEC za ta rufe rijistar masu zaɓe ranar Lahadi, 'yan adawa na neman a tsawaita lokacin rijistar