Nijeriya za ta gurfanar da mutum shida a kotu ciki har da wani janar mai ritaya da kuma wani tsohon minista bisa zarginsu da hannu a kitsa yi wa Shugaba Bola Tinubu juyin mulki.
An kama hafsoshi 16 game da "batutuwa na rashin ɗa’a" bayan rahotanni sun fito game da yunƙurin juyin mulki a watan Oktoban shekarar 2025.
Bayan haka ne Shugaba Tinubu ya cire manyan kwamandojin sojinsa a aiki kuma ya naɗa sabbin shugabannin sojin ƙasa da na sama da na ruwa.
Kafafen watsa labaran cikin ƙasar sun ruwaito ranar Talata cewa ofishin Antoni Janar na ƙasar ya kai ƙarar mutum shida bisa tuhume-tuhume 13 a kan juyin mulkin.
Tuhume-tuhumen ciki har da cin amanar ƙasa da ta’addanci da kuma gazawa wajen sanar da hukumomin tsaro game da juyin mulkin da aka kitsa da kuma halatta kuɗin haram mai alaƙa da ɗaukar nauyin ta’addanci, in ji rahotannin.
Cikin waɗanda aka bayyana a matsayin waɗanda aka kai ƙararsu kotun akwai tsohon ministan albarkatun man Nijeriya Timipre Silva, da janar mai ritaya Mohammed Ibrahim Gana da kyaftin ɗin sojin ruwa mai ritaya Erasmus Ochegobia Victor da kuma Ahmed Ibrahim, wani Sufeton ɗansanda.
Za a gurfanar da su ne ranar Laraba a gaban wata Babbar Kotu a babban birnin ƙasar, Abuja, in ji rahotannin.
Nijeriya ta fuskanci juyin mulki a wasu lokuta a tarihinta kuma ta shafe da yawa daga cikin shekarun ƙarni na 20 a ƙarƙashin mulkin soji tun lokacin da ta sami ‘yancin kai daga Birtaniya a shekarar 1960.
NIJERIYA
2 minti karatu
Nijeriya za ta gurfanar da janar mai ritaya da tsohon minista a kotu kan tuhumar su da juyin mulki
Kafafen watsa labaran Nijeriya sun ba da rahoton cewa ofishin Antoni Janar na ƙasar ya kai ƙarar mutum shida kan tuhume-tuhume shida game da zargin juyin mulki.
Rumbun Labarai
















