| Hausa
GABAS TA TSAKIYA
3 minti karatu
Yaƙin Iran da Isra'ila ya sa tafiya Umara zuwa Saudiyya na fuskantar barazana
Masu zuwa Saudiyya domin yin Umra na ƙaruwa a lokutan azumin watan Ramadan musamman zuwa ƙarshe-ƙarshen watan azumin.
Yaƙin Iran da Isra'ila ya sa tafiya Umara zuwa Saudiyya na fuskantar barazana
masu zuwa umra Saudiyya suna ƙaruwa a cikin azumin watan Ramadan, Musamman zuwa ƙrshen watan / Reuters
2 awanni baya

Ana fama da rashin tabbas a tsakanin masu tafiya Umara Saudiyya daga Nijeriya yayin da ake yaƙi tsakanin Amurka da Isra’ila da Iran yayin yaƙin ke ci gaba da shafar jigilar matafiya ta jiragen sama.

Masu zuwa Saudiyya Umara na ƙaruwa a lokacin azumin watan Ramadan musamman zuwa ƙarshe-ƙarshen watan azumin.

Sai dai kuma yaƙin da ake yi a Gbas Ta Tsakiya inda Amurka da Isra’ila suka fara kai hare-hare kan Iran, kuma ƙasar Iran take kai hare-haren ramuwar gayya da kuma rufe sararin samaniyar birane irin su Doha da Dubai, na tilasta wa masu taifiya Umara su sake shawara.

Yayin da wasu da suka riga suka tafi Umara kafin ɓarkewar rikicin ke tunanin komawa Nijeriya da wuri don gudun maƙalewa a can, wasu da ke da niyyar zuwa Umarar a Saudiyya suna sauya tunaninsu saboda rashin tabbas a Gabas Ta Tsakiya.

Ƙasashen Iran da Iraƙi da Isra’ila da Syria da Kuwait da Qatar da kuma Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa sun yi shelar rufe aƙalla wani ɓangare na sararrin samaniyarsu bayan Amurka da Isra’ila sun ƙaddamar da hare-hare a kan Iran, lamarin da ya katse jigilar matafiya ta sama cak.

Manyan kamfanonin jiragen saman da suka soke tafiya sun haɗa da Emirates da Etihad da Qatar Airways da Air France da British Airways da Syria Air da Air India da Turkish Airlines da EgyptAir da Lufthansa da Ethiopia Airlines.

Sai dai kuma wasu kamfanonin jiragen sama irin su kamfanin jiragen saman Saudiyya suna jigilar matafiya zuwa ƙasar har yanzu domin kawo yanzu Saudiyya ba ta rufe sararin samaniyarta ba tukunna a hukumance duk da hatsaniyar da ake yi a yankin.

Sararin samaniyar Saudiyya na ci gaba da karɓar jiragen sama masu jigilar fararen hula duk da tashin hankalin da ake yi a Gabas Ta Tsakiya.

Jaridar Daily Trust ta Nijeriya ta ambato wani maniyyaci daga Kano Alhaji Auwal Sani, wanda ya bayyana cewa an soke tashin jirginsa da a da zai tashi ranar Litinin.

“Da zan bi jirgin Qatar Airways ne, amma na samu saƙo daga gare su cewa an buɗe tikitin bayan an soke shi. Kuma kawo yanzu dai ba a bani biza ba, kuma na shirya tafiya da iyalina yau, amma duk mun maƙale. Allah ne ya san abin da ya fi mana,” in ji shi.

“Sun ce za a buɗa sararin samaniyar ranan 6 ga watan Maris, kuma za a ba mu biza domin mu yi tafiya,” in ji shi.

Kazalika jaridar ta ambato Salihu Shu’aibu, wanda ke da shrin tafiya Umara, inda ya ce lamarin ya sa shi cikin tashin hankali.