Gwamnatin Kano za ta sayi jirage marasa matuƙa don magance rashin tsaro a kan iyakokin jihar
Wannan matakin ya zo ne bayan jerin hare-haren da 'yan bindiga suka kai kwanan nan a Kananan Hukumomin Tsanyawa da Shanono.
Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya sanar da shirin sayen jiragen sama marasa matuƙa da kuma ƙarin kayan aiki na tsaro don ƙarfafa sa ido da kuma hanzarta ɗaukar mataki a kan iyakar jihar da Katsina.
Wannan matakin ya zo ne bayan jerin hare-haren da 'yan bindiga suka kai kwanan nan a Kananan Hukumomin Tsanyawa da Shanono.
An sanar da wannan shiri ne a wata sanarwa da mai magana da aywun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a ranar Laraba.
A cewar sanarwar, Gwamna Yusuf ya bayyana shirin ne yayin da yake tantance shirye-shiryen Rundunar Hadin Gwiwa (JTF) a sansanoninsu guda uku a fadin al'ummomin da abin ya shafa.
Gwamna Yusuf ya bukaci mazauna Tsanyawa da Shanono da su tallafa wa hukumomin tsaro da bayanai masu inganci da za su iya taimakawa wajen yaki da 'yan fashi. Ya kuma bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amsa bukatarsa ta neman tallafin tarayya a lokacin da ya kai ziyara Fadar Shugaban Ƙasa kwanan nan.
Gwamnan ya umarci JTF da ta ƙara himma wajen ceto mazauna da aka sace daga al'ummomin biyu. "Mun san cewa suna kai hari ga al'ummomin da ba su ji ba ba su gani ba, musamman a nan Tsanyawa da Shanono.
An kashe mutane da yawa da ba su ji ba ba su gani ba, sannan an sace wasu da dama," in ji shi, yana nuna damuwa game da irin hare-haren da ba a taɓa gani ba a Jihar Kano. "Da yardar Allah, za a mayar da waɗanda aka sace ga iyalansu."
Gwamna Yusuf ya tabbatar wa sojojin cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da fifita walwalarsu da kuma samar da tallafin da ya dace don inganta ayyukansu.
Ya bayyana hare-haren a matsayin "sabon abu" ga Kano kuma ya sake nanata alƙawarin gwamnatin jihar na yin aiki kafaɗa da kafaɗa da hukumomin tsaro don dawo da zaman lafiya.
A lokacin ziyarar tantancewa, gwamnan ya yi ta'aziyya ga iyalan da aka sace 'yan’uwansu, yana mai tabbatar musu da cewa ana ci gaba da ƙoƙarin ganin an sako su.
Rahotanni sun nuna cewa an sace kimanin mutum biyar a Tsanyawa da kuma wasu goma a Shanono, yayin da wata mace ta rasa ranta a lokacin hare-haren.
Gwamnati ta sake nanata ƙudurinta na magance ƙalubalen tsaro da ke tasowa da kuma kare mazauna yankunan da ke kan iyaka.