Jami'an tsaro sun ƙwace fasfon Nasir El-Rufa'i bayan yunkurin kama shi ya ci tura a filin jirgi

Mai taimaka wa tsohon gwamnan kan yada labarai Muyiwa Adekeye ya wallafa a shafinsa na X cewa a ranar Alhamis cewa "A yau jami'an tsaro sun so su kama Nasir El-Rufai bayan komawarsa gida daga birnin Cairo.

By
Jami'an tsaro sun kwace fasfon Nasir El-Rufa'i bayan yunkurin kama shi ya ci tura a filin jirgi

Jami'an tsaro a babban filin jirgin sama na Nnamdi Azikwe a Abuja sun ƙwace fasfon tafiye-tafiye na tsohon gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufa'i, jim kaɗan bayan saukarsa a Nijeriya daga Masar.

Mai taimaka wa tsohon gwamnan kan yada labarai Muyiwa Adekeye ya wallafa a shafinsa na X cewa a ranar Alhamis cewa "A yau jami'an tsaro sun so su kama Nasir El-Rufai bayan komawarsa gida daga birnin Cairo.

"El-Rafai ya ƙi bin su ba tare da an nuna masa takardar gayyata ba a hukumance, sai dai duk da haka sun ƙwace takardar fasfo dinsa daga hannun wani mai taimaka masa," in ji sanarwar.

Wani bidiyo da aka yi ta yaɗawa a shafukan sada zumunta ya nuna yadda Malam Nasir ke magana da wasu mutane a filin jirgin, inda yake cewa "idan kuna son ku gayyace ni ku ba ni takardar gayyata."

Lamarin na zuwa ne bayan da a ranar Laraba El-Rufai ya yi zargin cewa gwamnatin tarayya za ta iya kama shi, yana mai cewa alamu sun nuna abubuwan da ke faruwa a baya bayan nan shi ne zai zama mutum na gaba da ake hari. 

El-Rufai ya yi wannan zargi ne a yayin wata hira da DCL Hausa, yana mai nuna damuwa kan abin da ya bayyana a matsayin ƙaruwar barazanar siyasa ga abokan hamayya.

Tsohon gwamnan na Kaduna wanda ya bar APC mai mulki zuwa ADC ya ce tuni an kama wasu abokan hulɗarsa an tsare.