Shekaru da dama, gwamnatocin Amurka da suka biyo baya sun dage cewa mamaye yankin Gabar Yamma da Isra'ila ke yi zai lalata dokokin kasa da kasa kuma ya kashe yiwuwar zaman lafiya da za a iya cim ma wa.
Har ma Donald Trump ya bayyana a bainar jama'a cewa Isra'ila ba za ta hade yankin Gabar Yamma da yankinta ba bayan Yarjejeniyar Abraham.
Sakon da Washington ta fitar a bayyane yake: yayin da Amurka za ta iya jure wa gaskiyar da aka kirkira a kasa, hade yankin da Isra’ila ya ci gaba da zama batu mai muhimmanci.
Duk da haka, a wannan makon, wani hukunci mai cike da ce-ce-ku-ce da Ofishin Jakadancin Amurka da ke Kudus ya yi, ya nuna yadda ba a sake bukatar a ayyana hade yankin a matsayin wanda aka amince da shi ba.
A karon farko a tarihi, jami'an ofishin jakadancin Amurka za su samar da fasfo da ayyukan zama 'yan kasa a cikin matsugunai haramtattu da Isra'ila ta mamaye a yankin Gabar Yamma - za a fara daga Efrat sannan sai Beitar Illit.
Waɗannan ba ƙananan hukumomin Isra'ila ba ne da aka san su a cikin iyakar Isra'ila - matsugunan Yahudawa ne da aka kafa a cikin ƙasar Falasɗinu da aka mamaye wanda ya saɓa wa dokokin ƙasa da ƙasa, kuma mafi yawan al'ummomin duniya suna ɗaukar su a matsayin haramtattu.
Har zuwa yanzu, 'yan ƙasar Amurka da ke zaune a waɗannan matsugunan haramtattu ana buƙatar su yi tafiya zuwa wuraren diflomasiyya da aka amince da su a Yammacin Urushalima ko Tel Aviv don samun ayyukan ofishin jakadanci.
Wannan bambancin na da muhimmanci. Ya samar iyaka tsakanin Isra'ila da ƙasar da ta mamaye. Ketare wannan iyaka na canza wa fiye da yadda ake zato.
Matakin Amurka shi ne hari na baya-bayan nan da aka kai wa Gabar Yamma da mafarkin Falasɗinu na ƙasa mai iyaka da Isra’ila.
Kwanaki kaɗan da suka wuce, Isra'ila ta amince da shawarar yin rijistar filaye a Gabar Yamma da ta mamaye a matsayin "kadarori na ƙasa", wanda shi ne karo na farko tun lokacin da Isra'ila ta mamaye yankin Falasɗinu a shekarar 1967.
Me hakan ke nufi
Akwai dubban 'yan ƙasar Amurka da ke da takardun zama ‘yan kasar Isra'ila da ke zaune a matsugunan Gabar Yamma ba bisa ƙa'ida ba.
Bayar da ayyukan jakadanci a cikin matsugunai haramtattu kai tsaye yana shigar da waɗannan al'ummomi cikin ikon gudanar da ayyukan diflomasiyyar Amurka.
Wannan ba wai kawai isar da sako ga gwamnati ba ne. Faɗaɗa ayyukan gwamnati ne zuwa yankunan da ke ƙarƙashin mamayar sojoji a madadin fararen hula da ‘yan mamaya suka mayar zuwa wajen - hakan ya zama daidai yanayin abin da aka haramta a ƙarƙashin Mataki na 49 na Taro na Huɗu na Geneva.
Masu goyon bayan wannan matakin na iya jayayya cewa ayyukan jakadanci ba su da alaƙa da siyasa kuma suna wanzuwa don yi wa 'yan ƙasa hidima a duk inda suke zaune.
Amma a aikace, wannan yana iya haifar da daidaito tsakanin abin da jami'an Isra'ila da kansu suka ƙara bayyana wa a matsayin "ikon mallakar yankin Gabar Yamma da aka mamaye."
Mamaya da cinye ƙasa a ƙarni na 21 ba kasafai ke zuwa da sanarwa a hukumance ba.
A maimakon haka, mamayar na bayyana ta hanyar daidaita tsarin shari'a, gudanarwa, da kayayyakin more rayuwa a hankali tsakanin ƙasar da ke mamaye da yankin da take iko da shi. An faɗaɗa hanyoyi kuma.
An shigo da rajistar filaye. Hukumomin tsare-tsare sun haɗu. Kuma a ƙarshe, ayyukan gwamnati - gami da na gwamnatocin ƙasashen waje da ke da haɗin gwiwa - sun fara aiki ba tare da wata matsala ba a duk faɗin abin da aka taɓa fahimta a matsayin iyakar ƙasa da ƙasa.
Shawarar Washington ta tura ma’aikatan jakadanci zuwa matsugunan da suke ba bisa ƙa'ida ba ta dace da wannan manufar ta gudanarwa.
Kalaman Amurka na munafurci
Hakan kuma yana kawo wani babban sabani. Idan, kamar yadda jami'an Amurka suka sha faɗa, Amurka ba ta goyon bayan mamaye Gabar Yamma, me zai sa a ta kawo hanyar da za ta sauƙaƙa wannan mamayar?
Bayan haka, mamaya ba kawai doka ba ce. Tana da yanayin alƙaluman yawan jama’a da na matakan gwamnati.
Ana iya mamaye yanki ne a lokacin da rabuwar sa ta siyasa daga masu mamayar ta zama marar amfani da ake kallon ta tsufa - lokacin da tsarin gudanarwa, samar da ayyuka, da kariyar doka suka riga suka ɗauke ta a matsayin sararin cikin gida.
Ta hanyar bayar da ayyukan sabunta fasfo da na zama ɗan ƙasa a cikin matsugunan da ba bisa ƙa'ida, Amurka tana fuskantar hatsarin nuna cewa 'yan asalin Amurka da ke zaune a bayan iyakokin da Isra'ila ta amince da su ba sa yin hakan a cikin yanayi na siyasa, amma a matsayin wani ɓangare na yanayin farar hula na yau da kullum wanda ya cancanci tallafin diflomasiyya na yau da kullum.
Abubuwan da ke haifar da hakan sun wuce alamomin d aake gani da ido kawai.
A cikin dokokin ƙasa da ƙasa, an haramta canja wurin fararen hula na ƙasar da ke yin mamaya zuwa yankunan da aka mamaye saboda hakan na canza yanayin siyasa da yanayin al'umma na wannan yankin.
Ƙasashen da ke gefe sun taɓa ƙoƙarin guje wa duk wani mataki da zai iya amincewa ko taimakawa irin wannan sauya wurin zaman.
Bayar da ayyukan ofishin jakadanci a cikin matsugunan da ba bisa ƙa'ida yana tafiya ta bangare marar kyau - yana saka ayyukan ƙasashen waje cikin rayuwar yau da kullum na waɗannan al'ummomin.
Ga Falasɗinawa, wannan yana ƙarfafa damuwarsu da ta daɗe: cewa mamaye yankunansu ba ya gudana ta hanyar sanarwa ɗaya tilo, sai dai ta hanyar haɗin kai na gudanarwa - wanda, a wasu lokutan, ƙawayen Isra'ila mafi kusanci suka taimaka wajen tabbatar da shi.
Jami'an diflomasiyyar Amurka na iya dagewa cewa fasfo ba siyasa ba ce. Amma lokacin da aka bayar da waɗannan fasfo a cikin matsugunan da ba sa bisa ƙa'ida, layin da ke tsakanin hidimar ɗan ƙasa da amincewa da iyaka na da wahalar dore wa.
Washington ta ce tana adawa da mamayar. Duk da haka ta hanyar faɗaɗa tasirin diflomasiyya a cikin matsugunan da ba sa bisa ƙa'ida wanda zai sa a sami damar yin mamayar, yana iya taimakawa wajen samar da ainihin sakamakon da take iƙirarin ba ta kauna.















