| Hausa
WASANNI
2 minti karatu
An haramta wa ɗanwasan Ghana buga ƙwallo har abada saboda caca a Gasar MLS ta Amurka
An zargi Yaw Yeboah da shiga caca 'caca mai yawa' kan wasannin ƙwallo, ciki har da wasannin ƙungiyarsa a kakar 2024 da 2025.
An haramta wa ɗanwasan Ghana buga ƙwallo har abada saboda caca a Gasar MLS ta Amurka
Dan wasan tsakiya dan Ghana, Yaw Yeboah mai shekaru 20, yana murna bayan ya ci kwallo a kan Seattle Sounders. / REUTERS

Hukumar Gasar Ƙwallon Ƙafa ta Amurka, Major League Soccer (MLS), ta yanke hukuncin haramata wa ‘yanwasan ƙungiyar Columbus Crew su biyu buga wasa har abada, saboda laifin yin caca 'caca mai yawa'.

A ranar Litinin ne ɗanwasa ɗan asalin Ghana, Yaw Yeboah, da tsohon abokin wasansa a Columbus Crew, Derrick Jones suka samu wannan hukunci, kamar yadda sanarwar MLS ta nuna.

A halin yanzu, Yeboah da Jones, waɗanda suka kasance abokan wasa a Columbus Crew a 2024, ba su da kwantiragi da kowace ƙungiya.

Tun a Oktoba ne aka ba su hutun darakatarwa, yayin da ake gudanar da bincike kan zargin suna yin caca kan wasanni.

"Bayan nazarin sakamakon binciken, MLS ta tabbatar da cewa 'yan wasan sun shiga cikin caca mai yawa a kan wasannin ƙwallon kafa, ciki har da kan ƙungiyoyinsu, a kakar 2024 da 2025," in ji MLS a cikin sanarwar.

"A wani misali, dukkansu sun yi caca cewa Jones zai samu yalon kati a wani wasan ran 19 ga Oktoban 2024, wanda kuma ya samu."

'Samun bayanan sirri'

"MLS ta kuma gano cewa akwai yiwuwar 'yanwasan sun yaɗa bayanan sirri ga wasu masu caca game da niyyarsu na samun yalon katin," in ji hukumar, wadda yanzu ta shiga sahun masu fama da matsalar caca a Amurka bayan hukumar NBA da Major League Baseball.

"Babu wata shaida da aka gano da ta nuna cewa waɗannan ayyukan caca sun shafi sakamakon wani wasa," in ji MLS, inda kwamishina Don Garber ya ce hukumar "ta tsaya tsayin daka wajen tabbatar da sahihancin wasa."

Yaw Yeboah, mai shekaru 28, wanda ya buga wa ƙasarsa Ghana sau huɗu a 2021, na koma ƙungiyar Qingdao Hainiu ta kasar Sin a watan Fabrairu bayan fara ƙwallo a matakin ƙwararru tare da Manchester City.

Yeboah bai taɓa buga wasa a babbar tawagar Man City ba, sannan daga bisani an tura shi aro zuwa kulob-kulob a Faransa, Sifaniya da Belgium kafin ya koma MLS a 2022.

Jones, mai shekaru 29, an haife shi a Ghana amma ya wakilci Amurka a matakin ƙasa a tawagar ‘yan ƙasa da shekaru 23. Kafin buga wa Columbus, Jones ya yi wasa a Philadelphia Union, Nashville SC, Houston Dynamo, da Charlotte FC duka a Amurka.

Rumbun Labarai
Guardiola ya ce zai sallama Kofin Firimiya idan Man City ta sha kashi a hannun Arsenal
Nijeriya ta yi maraba da 'yarwasan tsere, Favour Ofili wadda aka hana ta sauya kasar da take wakilta
Shugaban FIFA ya ce akwai ‘tabbacin’ Iran za ta halarci Gasar Cin Kofin Duniya
Hukumar FA ta ci tarar Harry Maguire saboda rashin ɗa'a a wasan Man United da Bournemouth
UEFA ta yi watsi da korafin Barcelona kan wasan da Atletico Madrid ta doke su
Masoyin Arsenal ɗan Uganda na barazanar kai Gunners kotu kan damuwar da ya shiga bayan shan kaye
Danwasan Ghana, Kudus ya samu rauni a Tottenham, zai iya gaza zuwa gasar Kofin Duniya ta 2026
Anthony Joshua 'zai koma damben boksin' bayan mummunan hatsarin mota
Mbappe da Vinicius za su koma aiki tare a wasan Real Madrid da Bayern Munich
Ghana ta kori kocinta Addo makonni gabanin gasar cin kofin duniya
Ina Mo Salah zai koma daga Liverpool?
Nijeriya ta doke Iran a wasan sada zumunta da suka buga a Turkiyya
Lukaku ya ƙi komawa atisaye a Napoli bayan janyewa daga buga wa ƙasarsa Belgium wasa
Batun kofin AFCON: Me zai faru da ƙwallon ƙafa a Afirka bayan tataɓurza kan Senegal?
'Yanwasan Super Eagles 21 sun isa birnin Antalya na Turkiyya don wasannin sada zumunta
Mbeumo da Sesko na Man United ba za su je buga wa kasashensu wasan sada zumunta ba
Senegal za ta daukaka ƙara kan hukuncin ƙwace mata Kofin AFCON 2025
Tsohon golan Manchester United, Sergio Romero, ya yi ritaya daga kwallo
Joan Laporta ya sake zama shugaban Barcelona bayan lashe zaɓe
Trump ya sa tawagogin kasashen Afirka cikin matsala a gasar Kofin Duniya na FIFA 2026