| Hausa
NIJERIYA
3 minti karatu
Farashin saniya ya kai naira N2.5m, fiye da farashin mota a Legas, in ji mahauta
Kazeem ya alaƙanta tashin farashin da rashin tsaro da tashin kuɗin sufuri da kuma jinkiri da aka yi wajen aiwatar da shirye-shiryen gwamnatin jihar Legas na samar da wurin kiwon dabbobi na zamani.
Farashin saniya ya kai naira N2.5m, fiye da farashin mota a Legas, in ji mahauta
Mahauta a jihar Legas na kokawa game da tashin farashin saniya / Reuters
4 awanni baya

Ƙungiyar mahauta ta jihar Legas, babban birnin kasuwancin Nijeriya, ta yi ƙorafin yadda farashin saniya ke tashi babu ƙaƙƙautawa a jihar inda ya koma naira miliyan 2.5 daga naira miliyan 1.7 a shekarar 2025.

Jigo a ƙungiyar, Alhaji Bamidele Kazeem, shi ya bayyana wannan a wata tattaunawa da kamfanin dillancin labaran Nijeriya (NAN) ranar Lahadi a Legas.

Kazeem ya alaƙanta tashin farashin da rashin tsaro da tashin kuɗin sufuri da kuma jinkiri da aka yi wajen aiwatar da shirye-shiryen gwamnatin jihar Legas na samar da wurin kiwon dabbobi na zamani.

“Shanun da aka sayar kan naira miliyan 1.7 a shekarar da ta gabata a yanzu ana sayar da su tsakanin naira miliyan 2.3 zuwa naira miliyan N2.4. Akwai ma lokacin da aka sayar da wata saniya ɗaya naira miliyan 2.5 a kasuwar,” in ji shi.

Kazeem ya ce tashin farashin ya ƙara matsi kan mahauta da masu sayar da nama inda da yar masu sayar da nama da dama ke iya ci gaba da kasancewa a kasuwa.

“Motar da na saya a shekarar 2020 kan kuɗi naira miliyan 2.1 a yanzu ta fi araha kan kuɗin saniya ɗaya. Wannan ya nuna irin tsadar da shanu ke yi a halin yanzu,” in ji shi .

Ya koka cewa samun saniyar naira miliyan ɗaya a kasuwa a halin yanzu yana da wuya .

“Idan ka ga saniyar naira miliyan ɗaya, za ka yi mamaki . Abin da muka yi ƙorafi a kai a shekarar da ta gabata kaɗan ne idan aka kwatanta da abin da ke faruwa halin yanzu ,” a cewarsa .

Kazeem ya alaƙanta yanayin da rashin tsaron da ke addabar tafiyar dabbobi a sassan ƙasar da kuma ƙarin kuɗin mai da aka yi kwanan nan.

“An rage samar da shanun ne domin rashin tsaro a ƙasar da kuma ƙarin farashin man da aka samu kwanan nan wanda ya sa kudin mota ya tashi sosai,” in ji shi .

Ya ƙara da cewa ƙarin farashin man gas da man fetur sun sa farashin jigilar kayayyaki ya sake tashi musamman na dabbobin da ake kawowa daga arewacin Nijeriya, inda yawancin dabbobi ke shigowa kasuwannin Legas.

Kazeem ya ce masu kiwon dabbobi a yankin sun gaza cike giɓin dabbobin domin har yanzu labin dabbobi (wuraren ciyar da dabbobi) da ma shirye-shiryen tirke dabbobi na zamani bai kankama ba tukunna a Legas.

“Masu kiwo a wannan yankin ba sa iya biyan buƙatar da ake na dabbobin domin labin shanu da shirye-shiryen kiwon shanu na zamani na gwanatin jihar ba su kankama ba tukunna, Har yanzu mun dogara ne sosai kan masu samar da shanu daga jihohin arewaci,” in ji shi.

Ya yi kira ga gwamnatin ta gaggauta ƙaddamar da shirin Kiwo na Eko a Gbodu, da ke garib Epe, na jihar yana mai cewa shirin zai ƙara yawan shanun da ake samu da rage kudin jigilar shanu da kuma rage farashin nama.

“Riban tirke dabbobi na da yawa . Zai samar da ayyukan yi ga matasanmu kuma zai iya sauƙar da farashin nama,” in ji shi.