Wata makala da aka wallafa a wata jaridar Isra'ila ta ba da shawarar cewa ya kamata Amurka ta yafe wa matasan Amurkawa basussukansu idan suka amince su shiga shirin kai hari ko mamaye Iran, inda marubucin ke cewa ba za a iya cin nasarar yaƙin Amurka da Iran ta hanyar kai hare-haren sama kaɗai ba, sai dai an mamaye ko kuma an karɓe iko da ƙasar, lamarin da zai buƙaci tattara sojoji har miliyan 1.5.
AJ Jaff, wani tsohon jami'in Rundunar Sojin Canada mai ritaya ne ya gabatar da wannan shawara mai tayar da hankali ta amfani da matasan Amurkawa masu basussuka a matsayin sojojin da za a aika fagen daga da Iran, a cikin wata makalar ra'ayi da ya wallafa a jaridar Jerusalem Post.
A cikin hujjojinsa, Jaff ya ce hare-haren Amurka masu tsanani da aka kwashe watanni ana kai wa Iran ba su durƙusar da ƙarfin sojin Iran ba, kuma ba su kawo ƙarshen yaƙin ba. Ya ce mamayar ƙasa za ta buƙaci sojojin Amurka da suka fi ƙarfin waɗanda take da su a yanzu nesa ba kusa ba.
"Adadin masu shiga aikin soja yana ƙasa da abin da mamayar ƙasar Iran za ta buƙata. Ƙiyasin da ake yi na samun nasarar yaƙin ƙasa da ƙasa kan rundunonin larduna 31 na Iran da kuma tsarin tsaronta na Mosaic Defense Doctrine ya kai tsakanin sojojin Amurka 750,000 zuwa miliyan 1.5. A halin yanzu, Rundunar Sojin Ƙasa ta Amurka tana da kusan sojoji 452,000. Babu shakka, lissafin bai yi ba," in ji marubucin.
Jaff ya ce tarihin Amurka na iya nuna wata hanya da za a bi: ɗaukar mutane aikin soja ta hanyar shirin yafe basussuka maimakon tilasta musu shiga aikin soja a lokacin yaƙi.
"Talakan Amurka mai shekaru 18 zuwa 34 yana ɗauke da basussukan da ba na jinginar gida ba da suka fi dala 40,000, ciki har da basussukan karatu, basussukan katin kuɗi, basussukan motoci da kuma rance na kai, yayin da wasu ƙiyasi suka kai har dala 100,000," in ji shi, yana ƙarawa da cewa wannan shi ne rukunin mutanen da Pentagon ke buƙata.
Jaff ya ce: "Shirin ɗaukar mutane aikin soja da gwamnatin tarayya ke gudanarwa, wanda zai yafe gaba ɗaya basussukan karatu, katin kuɗi da sauran rance bayan watanni 24 ko 36 na aikin soja, tare da faɗaɗa tsarin GI Bill, zai sa adadi mai yawa na mutane su shiga aikin soja don raɗin kansu."
Shawara mai ban mamaki
Kusan kashi 77 cikin 100 na Amurkawa suna da wani nau'i na bashi. Wannan na nufin kusan mutane miliyan 250 zuwa 260 suna fuskantar nau'o'in basussukan kuɗi daban-daban, lamarin da ya taimaka wajen kai jumullar basussukan gidajen Amurka zuwa wani tarihi na dala tiriliyan 18.8. Manya a Amurka suna ɗauke da matsakaicin bashin kusan dala 63,500.
Jaff ya kawo wasu misalai daga tarihin Amurka na irin waɗannan shirye-shiryen ɗaukar sojoji, yana mai cewa Yaƙin Duniya na Biyu ya haifar da tsarin GI Bill, yayin da Yaƙin Vietnam ya ba ɗalibai damar jinkirta shiga aikin soja.
"Yaƙe-yaƙen da aka yi bayan 11 ga Satumba sun bayar da garaɓasa ga masu shiga aikin soja da kuma hanyoyin samun zama ɗan ƙasa. Yaƙin Iran zai buƙaci bayar da rangwamen bashi. Yanayin tattalin arzikin Amurkawan da ke ɗauke da basussuka masu shekaru 20 zuwa 30 ya sa wannan ya zama hanya mafi inganci da Pentagon da gwamnatin Trump za su iya amfani da ita wajen samun sojoji," kamar yadda marubucin ya jaddada.
Jaff ya ya bayyana shirin a matsayin wanda hankali ba ya ɗauka amma kuma ya bayyana shi a matsayin "hanyar da ta fi inganci" da Pentagon da gwamnatin Trump za su iya amfani da ita, yana mai cewa ƙasashe suna ɗaukar sojoji ta hanyar tsara abubuwan ƙarfafawa da suka dace da al'ummominsu.
Makalar Jaff ta gabatar da wannan shiri mai tayar da hankali a matsayin ɗaya daga cikin hanyoyi uku da ba na amfani da ƙarfi kai tsaye ba da Washington za ta iya amfani da su wajen kayar da Iran, tare da amincewar Majalisar Dokokin Amurka da 'yancin kan ƙananan kabilun Iran da kuma cim ma yarjejeniya da China kan man fetur ɗin Iran.
Makalar ta jawo suka mai yawa, inda mutane da dama suka yi watsi da shawarwarin a matsayin marasa inganci daga mahangar Amurka, wasu kuma suke saka ayar tambaya kan ƙwarewar marubucin. Wasu kuma sun yi zargin cewa Isra'ila na son ci gaba da yaƙi da Iran "har zuwa lokacin da Amurkawa na ƙarshe za su mutu."
Kafafen yaɗa labarai kamar The Blaze sun bayyana shawarar a matsayin amfani da bashin da Amurkawa ke ciki ko kuma dabarar yaudara. Ta bayyana shirin Jaff a matsayin shawara mai ban mamaki ta tura matasan Amurkawa masu fama da bashi zuwa sahun gaba na fagen daga.
Cibiyar Mises Institute ta yi wa bayaninta taken "Jerusalem Post na kira ga ƙarin Amurkawa su shiga aikin soja – domin su mutu saboda Isra'ila", inda ta bayyana makalar a matsayin kiran wata kafar yaɗa labarai ta Isra'ila ga masu biyan haraji a Amurka da su ɗauki nauyin wani yaƙi.

















