Shugaban Hukumar Sadarwa na Turkiyya, Burhanettin Duran ya yi kira ga ƙasashen Musulmai da su haɗa kai wajen ba da labarinsu da kansu, yana mai gargaɗin cewa tsarin ƙasa da ƙasa na fuskantar rikicin da rashin adalci da ba a taba ganin irinsa ba, kuma wadanda suka gina shi a yanzu suna cikin manyan masu kawo cikas ga tsarin.
A jawabin da ya gabatar a taron Tasirin Musulmai na 2026 a Istanbul, Duran ya ce duniya tana cikin wani gagarumin sauyi wanda ya wuce canjin da aka gani a shekarun baya.
"Yaƙe-yaƙe, kisan kare dangi, annoba da kuma rugujewar aminci ga cibiyoyi da dokokin ƙasa da ƙasa sun nuna a fili cewa an take wani muhimmin mataki," in ji shi, yana mai kara da cewa ƙasashen duniya ba su da wani hangen nesa game da makomar gobe.
Duran ya yi nuni kan abin da ya bayyana a matsayin manyan alamu na rugujewar tsarin, yana mai cewa manyan ƙasashe suna yin kasa a gwiwa wajen daukar alhaki sannan wasu daga cikin wadanda suka kafa tsarin duniya sun zama manyan masu kawo cikas a cikinsa.
Ya ƙara jaddada irin raunin tasirin cibiyoyin da aka ƙirƙira don kiyaye zaman lafiya da kuma warware rikice-rikice.
Kazalika ya ce an samu irin wannan sauyin a bangaren sadarwa, yana mai kari da cewa a yanzu duniya ta sauya daga ‘‘zamanin tattauanawa’’ zuwa abin da ya kira zamanin labarai.’’
"A wannan sabon zamani, gasar ba ta takaita ga labarai kawai ba, ta shafi har yadda ake tsara gaskiya, fahimta, da kuma yadda ra'ayoyin jama’a suke ga kasashen duniya,’’ in ji Duran.
Ya kuma ƙara da cewa, a yayin da a yanzu saƙonni suke iya isa ga mutanen duniya cikin kankanin lokaci, saurin yana da tafe da haɗura na yada labaran labaran ƙarya da yaudara da kuma rashin iya tsage gaskiya da ƙarya.
Duran ya ce, ba a takaita rikice-rikice a fagen daga kawai ba, har ta hanyar fahimta da bayanai ana fafatawa.
Ya yi gargaɗin cewa bidiyoyin karya, da abubuwan da aka shirya su na ƙarya da kuma kafofin sadarwa na farfaganda da tsara sun zama kan gaba wajen haifar da rikicin zamani.
"A matsayinmu na Hukumar Sadarwa, muna ganin kafa tsarin labarai bisa ga ingantattun bayanai, waɗanda aka tabbatar kuma aka dogaro akansu a matsayin ɗaya daga cikin babban abin da muka fi mayar da hankali akai," in ji shi.
Da yake nuna rawar da Turkiyya ke takawa a harkokin ƙasashen duniya, Duran ya ce ƙasar ta yi aiki a matsayin mai shiga tsakani kana mai gina zaman lafiya a manyan rikice-rikice da dama, ciki har da na Iraki, da Siriya, da Kudancin Caucasus,da Ukraine da kuma Gaza.
Ya ce saƙon Shugaba Recep Tayyip Erdogan cewa "duniya ta fi girman iya ƙasashe biyar" martani ne kai tsaye ga rashin daidaiton manufofi a tsarin duniya.
Al'ummomin Musulmai a matsayin masu tsara dokoki
Burhanettin Duran ya kuma soki wariyar da ake nuna wa al'ummomin Musulmai wajen tsara dokokin duniya, yana mai cewa galibi an cire su daga yanke shawarwari da dokoki lokacin da aka kafa tsarin shekaru da yawa da suka gabata.
Ya yi misali da aikin Edward Said, musamman na ‘Orientalism da Covering Islam,’ yana mai nuni da cewa labaran Yamma sun daɗe suna tsara yanayin fahimtar duniya game da Musulunci.
Shugaban Hukumar Sadarwa na Turkiyya ya ce dole ne al'ummomin Musulmai su wuce matsayin kariya da abin da ya bayyana a matsayin tunanin da ƙasashen Yamma suka sanya, a madadin haka su zama masu tsara dokoki a cikin tsarin duniya mai tasowa.
"Sauyin zamanin yanzu ba wai kawai yana gabatar da haɗari ba ne har ma da damammaki," in ji shi.
"Dole ne mu dawo da dabi'unmu cikin tsarin kuma mu shawo kan hanyoyin kariya da kyamar Musulunci da kuma ra'ayoyin da ƙasashen Yammacin duniya suka tsara."
Duran ya jaddada rawar da kamfanonin fasaha, kungiyoyin fafutuka da na leken asiri da ma kafofin sadarwa na zamani da ba su da sahihanci suke takawa wajen tsara labaran duniya, yana mai cewa suna tasiri ga rikice-rikice da kuma muryoyinsu waɗanda ake son jin su.
Haka kuma, ya ce wannan yanayi yana ba da dama ga al'ummomin Musulmai su dawo, su kuma bayyana labaransu.
"Idan ba za mu iya ba da labarinmu ba, wasu za su ci gaba da taya mu ba da labarin," in ji shi.
"Kuma idan wasu suka ba da labarinmu, za su ayyana matsayinmu a duniya."
Ya yi kira da a kara karfafa haɗin gwiwa tsakanin gwamnatoci, ƙungiyoyin fararen hula, masana ilimi, 'yan jarida da masu fasaha, tare da kara zuba jari a fannin ilimin zamani da cibiyoyi don yaƙi da labaran karya.
Duran ya bayyana fatan cewa tattaunawa da kuma haɗin gwiwar da aka samu a taron zai karfafa haɗin kai a faɗin ƙasashen Musulmai kuma zai ba da gudummawa mai kyau ga al'ummar duniya baki ɗaya.
















