Pentagon na shirya jadawalin ayyukan sojin ƙasan Amurka na tsawon makonni a Iran — Rahoto
Jami'ai sun ce waɗannan tsare-tsaren alamu ne na wani sabon “mataki na yaƙin” wanda zai iya zama “mai haɗari sosai” ga rundunar Amurka fiye da haɗarin da suka shiga a makonni huɗun farko na yaƙin.
Hedkwatar Tsaro ta Amurka wato Pentagon ta shirya tsare-tsare na yiwuwar ayyukan sojojin ƙasa na tsawon makonni a Iran yayin da aka tura dubban sojojin Amurka zuwa Gabas ta Tsakiya inda a halin yanzu ake jiran yanke shawarar Shugaba Donald Trump, a cewar rahoton The Washington Post.
Jami'ai sun ce waɗannan tsare-tsaren alamu ne na wani sabon “mataki na yaƙin” wanda zai iya zama “mai haɗari sosai” ga rundunar Amurka fiye da haɗarin da suka shiga a makonni huɗun farko na yaƙin, a cewar The Washington Post.
Duk wani aiki da sojojin ƙasa za su yi ba zai zama mamayar ƙasar baki ɗaya ba, kuma zai iya haɗawa da farmaki na dakaru na musamman da rundunar sojojin ƙasa na gargajiya, in ji jami'an da suka yi magana ba tare da bayyana sunayensu ba.
Sun ce ayyukan na iya sanya sojoji cikin haɗari daga hare-haren “jirage marasa matuƙa da makamai masu linzami, luguden wuta da bindigogi da gurneti”.
“Aikin Pentagon ne ya shirya domin bai wa shugaban ƙasa zaɓuɓɓuka da yawa,” in ji kakakin Fadar White House Karoline Leavitt, a cewar rahoton. “Ba yana nufin Shugaban ya yanke shawara ba.”
Tattaunawar sun haɗa yiwuwar ayyuka a Tsibirin Kharg, muhimmiyar cibiyar fitar ɗanyen mai ta Iran, da farmakin bakin teku kusa da Tashar Hormuz don rage barazanar da ke kan jigilar kaya.
Jami'ai sun ce yiwuwar waɗannan ayyuka na iya ɗaukar “makonni, ba watanni ba, yayin da wasu suka kiyasta watanni kaɗan.”
Trump ya ce, “Ba zan tura sojoji ko'ina ba,” yayinda Sakataren Harkokin Waje Marco Rubio ya ce wannan “ba zai zama dogon rikici ba” kuma za a iya cim ma buri “ba tare da sojojin ƙasa ba.”
An ce an kashe sojojin Amurka goma sha uku kuma fiye da 300 sun ji rauni a hare-hare a faɗin yankin tun bayan da yaƙin Amurka da Isra'ila kan Iran ya fara a ƙarshen Fabrairu.
Ƙaruwar tashin hankali a yankin ya ci gaba tun lokacin da Isra'ila da Amurka suka ƙaddamar da farmaki kan Iran a ranar 28 ga Fabrairu, wanda ya hallaka fiye da mutane 1,300 zuwa yanzu, ciki har da Jagoran Addini na ƙasar Ali Khamenei, a cewar rahotanni.
Iran ta mayar da martani da hare-haren jiragen sama marasa matuƙa da makamai masu linzami masu zuwa Isra'ila da Jordan da Iraƙi da kasashen Gulf da suka kasance masaukin kayan aikin soja na Amurka.