ECOWAS ta yi tir da ikirarin ‘ƙarya mai hatsari’ na Amurka cewa Nijeriya ta bari ana kashe Kiristoci
Hare-haren ta’addanci a yankin na afka wa kan fararen hula mabiya dukkan addinai ne ciki har da Musulmi, in ji Ƙungiyar raya tattalin arziƙin ƙasashen yammacin Afirka (ECOWAS).
Ƙungiyar raya tattalin arziƙin ƙasashen yammacin Afirka (ECOWAS) Talata ta yi watsi da “[murya mai ] ƙarfi” da zarge-zargen Amurka cewa Nijeriya ta bari ana kashe Kiristoci.
Ƙungiyar yammacin Afirka ta yi watsi da “iƙirarin na ƙarya mai hatsari wanda ke neman zurfafa rashin tsaro cikin al’ummomi da kuma raunana haɗin kai na zamantakewa a yankin,” kamar yadda ta bayyana a wani saƙon da ta wallafa a shafin X.
Wannan na zuwa ne bayan Shugaban Amurka Donald Trump ya wallafa a shafinsa na Truth Social ranar Asabar cewa idan gwamnatin Nijeriya ta "ci gaba da bari ana kashe Kiristoci," Washington za ta yanke dukkan agaji.
Trump ya ce Amurka za ta iya “shiga cikin waccar ƙasar wadda a yanzu ta kunyata, 'da bindigogi masu wuta.’”
ECOWAS ta ce hare-haren ta’addanci a yankin na afkawa ne kan fararen hula na dukkan addinai, ciki har da Musulmai da Kiristoci da kuma mabiya sauran addinai kuma rahotanni masu zaman kansu tun a shekarun da suka gabata sun nuna cewa hare-haren ba sa bambanta tsakanin jinsi da addini da ƙabila ko kuma shekaru.
ECOWAS ta yi kira ga MDD da dukkan abokan hulɗa su tallafa wa mambobinta wajen yaƙi da ta’addanci da kuma "ɗaukawa a matsayin ƙarya duk wani iƙirarin cewa waɗannan ƙungiyoyin ta’adancin suna afka wa wasu mutane ɗaya ne kawai ko kuma cewa akwai kisan kiyashi kan wasu mabiya addini ɗaya a yankin."
Ta yi kira ga duniya ta goya wa ƙasashen yammacin Afirka baya a yaƙinsu da ta’addancin da ke addabar “dukkan al’ummomi.”