| Hausa
AFIRKA
3 minti karatu
Fafaroma Leo ya fara ziyararsa ta farko zuwa Afirka
Fafaroma Leo zai kwashe kwana 11 a ziyararsa ta farko zuwa Afirka inda zai je ƙasashe huɗu.
Fafaroma Leo ya fara ziyararsa ta farko zuwa Afirka
Pope Leo na XIV ya fara tafiyarsa ta manzanci ta farko zuwa Aljeriya da Angola da Kamaru da kuma Equatorial Guinea / Reuters
5 awanni baya

Fafaroma Leo na XIV ya isa ƙasar Aljeriya ranar Litinin a ziyararsa ta farko a nahiyar Afirka da zummar ƙarfafa zaman tare tsakanin Musulmai da Kiristoci a wani lokaci da duniya ke fama da rikici.

Fafaroma Leo zai kwashe kwana 11 a ziyarar tasa inda zai je ƙasashe huɗu — Aljeriya da Kamaru da Angola da kuma Equatorial Guinea.

Shugaban Aljeriya Abdelmadjid Tebboune ya tarbi Fafaroma Leo a filin jirgin sama na ƙasa da ƙasa na birnin Algiers kuma daga bisani za su gana a fadar shugaban ƙasa ta El Mouradia .

Daga baya ranar Litinin, Leo zai gabatar da jawabi ga hukumomin Aljeriya da kuma kai ziyara babban masallacin birnin.

Zai kuma ƙarƙare ranar da wani taro a cocin Our Lady of Africa basilica, sannan zai yi addu’o’i a wajen tunawa da wasu ‘yan ci-rani da suka mutu sakamakon kifewar jirgin ruwa yayin da suke ƙoƙarin zuwa Turai.

Saƙonnin zaman lafiya

Taken ziyarar ta Ajleriya shi ne abin da Leo ke faɗa duk inda ya je — “sallama a gare ku” — kuma Fadar Vatican ta ce saƙon salama da kuma zama tare tsakanin Kiristoci da Musulmai zai kasance muhimmin abin da ziyarar zai mayar da hankali a kai.

A Aljeriya, wata ƙaramar al’umma ta katolika wadda ke da kimanin mutum 9,000 waɗanda yawancinsu baƙi ne suna zama tare da Musulmai da suka fi rinjaye waɗanda suka kai miliyan mutum 47, in ji ƙididdigar Vatican.

Babban Bishop na birnin Algiers, Cardinal Jean-Paul Vesco ɗan Faransa, ya ce a ko wace rana, mutum tara daga cikin 10 da ke zuwa basilica ɗin Musulmai ne.

“Abin burgewa ne mutum ya iya nuna cewa za mu iya zama kasancewa ‘yan’uwa maza da mata tare, masu gina wata al‘ulmma ɗaya duk da bambancin addinanmu ,” kamar yadda Vesco ya shaida wa kamfanin dillancin labaran The Associated Press ranar jajiberen isowar Leo. “Kuma shi ne abin da cocinmu ke ta yi tun lokacin da wannan ƙasar ta samu ‘yancin kai.”

‘Yancin addini

Kundin tsarin mulkin Aljeriya ya yarda da “wasu addinan da ba Musulunci ba ” kuma ya bai wa mutane damar yin addininsu.

A ranarsa ta farko a Aljeriya, Leo zai gabatar da saƙon girmamawa ga Kiristoci 19 da suka yi shahada da kuma kai ziyara ga mata masu zuhudu na Augustine da ke hidima a basiilaca ɗin Algiers inda suke taimaka wa mutanen dukkan addinai.

An bayyana dukkansu 19 a matsayin shahidai da suka mutu domin addinin ne a shekarar 2018, irin wannan abin da aka fara yi a karon farko a duniyar Musulmi.

Ranar Talata, Leo zai ziyarci birnin Annaba, wanda a zamanin yanzu ake kira Hippo, inda wani mashahurin waliyin ɗarikar Katolika, Augustine, ya kasance Bishop na tsawon shekara talatin.