Bayan wasa ɗaya kacal a gasar Kofin Duniya, Tunisia ta sallami kocinta, Sabri Lamouchi, sakamakon lallasawar da Sweden ta musu a wasansu na farko a gasar Kofin Duniya na FIFA 2026.
Wasan nasu na Rukunin F ya gudana ranar Lahadi, inda da ƙyar suka sha da ƙwallo ɗaya, yayin da Sweden ta zura musu ƙwallaye 5 rigis, mafi munin sakamakon da suka samu.
Rahotannin na cewa Hukumar Ƙwallo ta Tunisia, FTF, ta soke kwantiraginsa nan-take, duk da cewa da ma zaman Lamouchi, ɗan asalin Faransa a ƙungiyar bai yi wani armashi ba.
Sallamar na zuwa ne bayan wasanni biyar kacal yana riƙon tawagar, inda ta bayyana cewa akwai ɓaraka tsakanin masu horar da ‘yanwasa da kuma kocin.
Bayan tafiyar Lamouchi, ana sa ran tawagar da ake kira “Carthage Eagles” za ta koma ƙarƙashin riƙon tsohon kocinsu, Mondher Kebaier, don riƙon ƙwarya.
A ranar Asabar, 20 ga Yuni Tunisia za ta kara da Japan a wasansu na biyu, bayan da ƙasar ta zama ta farko da ta raba gari da kocinta sakamakon gasar Kofin Duniya da ke gudana a Amurka, Canada, da Mexico.




.jpeg?width=512&format=webp&quality=80)






