Kungiyoyi 5 na neman Lewandowski duk da shekarunsa 37
Tuni rahotanni suka ce ƙungiyoyi biyar a ciki da wajen Turai sun fara yunƙurin ɗauko Robert Lewandowski daga Barcelona, saboda har yanzu gwani ne shi wajen zura ƙwallo.
Yayin da ƙarshen kwantiraginsa a Barcelona ke ƙaratowa, tauraron ɗanwasa Robert Lewandowski yana ƙara samun farin jini a wajen ƙungiyoyi a ciki da wajen nahiyar Turai.
Ɗanwasan ɗan asalin Poland ya fara samun tayi daga maƙwabciyar ƙungiyarsa ta birnin Madrid a Sifaniya, wato Atletico Madrid.
Daga Italiya ma AC Milan na kwaɗayin ɗauko ɗanwasan, sannan akwai Fenerbahce daga Turkiyya, baya ga ƙungiyoyi a Amurka da Saudiyya da suka shirya farauto shi.
Ranar 30 ga Yunin shekarar nan ta 2026 ne kwantiragin Lewandowski za ta ƙare a Barcelona, wanda ke nufin ƙungiyoyin da ke zawarcinsa za ma su iya samun ɗaukar sa a kyauta.
Duk da cewa shekarun Lewandowski 37, yana da tagomashin zura ƙwallo a duka ƙungiyoyin da ya taka keda, don haka har yanzu ana kallonsa a matsayin abin nema.
Zaɓen shugaban Barcelona
Sai dai duk da tarin masu zawarcinsa sa, rahotanni na cewa Robert Lewandowski ba a matse yake ba ya zaɓi wajen zuwa.
Hasali ma an ce ya yanke hukunci kan matakinsa na gaba, kuma ba zai sanya hannu kan wata takardar alƙawari gabanin sabuwar kwantiragi ba, sai nan da Afrilu.
Babban dalilin jinkirta hukuncin nasa ba ya rasa nasaba da siyasar zaɓen shugabannin gudanarwar Barcelona, wanda za a yi a ranar 15 ga Maris.
Sakamakon wannan zaɓen na shuwagabannin zai haska makomar ƙungiyar a kaka mai zuwa ta 2026-27, da ma shekaru masu zuwa.