Gabon ta dakatar da wasu shafukan sada zumunta, inda ta bayyana cewa wasu saƙonnin da ake wallafawa ka iya zama barazana da hukumomi da tsaron ƙasar, kamar yadda hukumar da ke sa ido kan sadarwa ta ƙasar ta sanar a wata sanarwa.
Hukumar Sadarwa ta Gabon ta bayar da umarnin dakatarwar nan take "har sai baba-ta-gani," ba tare da fayyace waɗanne shafukan matakin ya ɗauka ba.
Kungiyar da ke sa ido kan intanet NetBlocks a ranar Laraba ta ce an dakatar da shafukan Meta da YouTube da TikTok a Gabon. sa
Hukumar Sadarwa ta Gabon ta ce ‘yan gwagwarmaya na amfani da shafukan sada zumuntan don saɓa dokokin Gabon ta hanyar yaɗa “abubuwa marasa kyau na cin mutunci da ƙiyayya.”
An zaɓi Shugaban Gabon, Brice Oligui Nguema, a Afrilun bara, bayan ya jagoranci juyin mulki a Agustan 2023 wanda ya kawo ƙarshen mulkin fiye da shekaru 50 na tsohon shugaban ƙasa Ali Bongo.












