| Hausa
WASANNI
2 minti karatu
Tottenham na neman masanin lafiyar tunani ga ‘yanwasanta, don gujewa fadowa daga gasar Firimiya
Sabon kocin Tottenham, Roberto De Zerbi ya gano cewa ƙungiyar na fama da raunin zuciya, inda yake jaddada buƙatar ƙarfafa zuciya.
Tottenham na neman masanin lafiyar tunani ga ‘yanwasanta, don gujewa fadowa daga gasar Firimiya
Tottenham na cikin ƙungiyoyin ƙwallo shida mafi girma a Ingila / Reuters

Tottenham Hotspur ta saka tallan neman sabon masanin lafiyar tunani don warkar da matsalar da ‘yanwasanta ke ciki ta rashin karsashi yayin da suke tararrabin faɗowa daga gasar Firimiya, zuwa ƙaramar gasar Championship ta Ingila.

A halin yanzu Tottenham, wadda ake lissafawa cikin manyan ƙungiyoyi shida na Ingila, tana cikin ƙungiyoyi uku na ƙasan teburin Firimiya.

Dole ne ƙungiyar ta lashe wasanni biyar da suka rage mata a kakar bana, don fatan tasowa sama cikin ƙungiyoyi 17 na saman teburi don kauce wa babban ƙalubalen rikitowa daga Firimiya.

Tun shigowar 2026, Spurs ba ta yi nasara a ko da wasa guda ba, wanda ya janyo mahukunta tunanin cewa rashin karsashi ya shiga zukatan ‘yanwasan har a cikin fili.

Rahotanni na cewa a halin yanzu Tottenham tana neman jami’in da ya ƙware wajen iya ƙara ƙwazo. Hakan na nuna cewa mahukuntan suna ganin kyautata taka ƙwallo kacal ba zai warkar da matsalarsu ba.

Sanarwar neman masanin lafiyar tunanin ta fayyace abubuwan da ake buƙatu wajen masanin, tana cewa, “Muna neman fitaccen masanin tunani, gwanin wajen ƙara ƙwazo don ya shigo tawagarmu ta ƙara ƙwazo”.

Sabon kocin Tottenham, Roberto De Zerbi ya gano cewa ƙungiyar na fama da raunin zuciya, inda yake jaddada buƙatar ƙarfafa zuciya.

Ya faɗa a wasansu na ƙarshe inda suka yi 2-2 da Brighton, "Ina alfahari da ƙwazon su, suna buƙatar nuna ƙarin jajircewa da mayar da hankali kan wasanmu da Wolverhampton, kuma su zo filin atisaye ranar Litinin da murmushi….”

Rumbun Labarai
Hukumar FA ta ci tarar Harry Maguire saboda rashin ɗa'a a wasan Man United da Bournemouth
UEFA ta yi watsi da korafin Barcelona kan wasan da Atletico Madrid ta doke su
Masoyin Arsenal ɗan Uganda na barazanar kai Gunners kotu kan damuwar da ya shiga bayan shan kaye
Danwasan Ghana, Kudus ya samu rauni a Tottenham, zai iya gaza zuwa gasar Kofin Duniya ta 2026
Anthony Joshua 'zai koma damben boksin' bayan mummunan hatsarin mota
Mbappe da Vinicius za su koma aiki tare a wasan Real Madrid da Bayern Munich
Ghana ta kori kocinta Addo makonni gabanin gasar cin kofin duniya
Ina Mo Salah zai koma daga Liverpool?
Nijeriya ta doke Iran a wasan sada zumunta da suka buga a Turkiyya
Lukaku ya ƙi komawa atisaye a Napoli bayan janyewa daga buga wa ƙasarsa Belgium wasa
Batun kofin AFCON: Me zai faru da ƙwallon ƙafa a Afirka bayan tataɓurza kan Senegal?
'Yanwasan Super Eagles 21 sun isa birnin Antalya na Turkiyya don wasannin sada zumunta
Mbeumo da Sesko na Man United ba za su je buga wa kasashensu wasan sada zumunta ba
Senegal za ta daukaka ƙara kan hukuncin ƙwace mata Kofin AFCON 2025
Tsohon golan Manchester United, Sergio Romero, ya yi ritaya daga kwallo
Joan Laporta ya sake zama shugaban Barcelona bayan lashe zaɓe
Trump ya sa tawagogin kasashen Afirka cikin matsala a gasar Kofin Duniya na FIFA 2026
Barcelona za ta ƙwato Haaland daga Manchester City don maye gurbin Lewandowski
Courtois ya jajanta wa golan Tottenham da aka ci ƙwallo 3 a minti 16 da fara wasa
Ƙwallon da Galatasaray ta zura a raga a farkon wasa ya nutsar da Liverpool a karawar Zakarun Turai