| Hausa
AFIRKA
2 minti karatu
An miƙa wa 'yan kwangila ayyukan fara gina azuzuwa 357 a jihar Dosso ta Nijar
Kamfanin dillancin labaran Nijar ANP ya ruwaito cewa an yi bikin miƙa ayyukan ne a wani taro da manyan jami’an gwamnati da wakilan kamfanonin ‘yan kwangila suka halarta a jihar.
An miƙa wa 'yan kwangila ayyukan fara gina azuzuwa 357 a jihar Dosso ta Nijar
Gwamnan jihar Dosso, Kanal-Manjo Bana Alhassane, ne ya jagorancin bikin ranar Jumma'a a makaranatr firamare ta Banizoumbou da ke Dosso

Gwamnan jihar Dosso a Jamhuriyar Nijar, Kanal-Manjo Bana Alhassane, ya miƙa ayyukan gina azuzuwa 357 ga ‘yan kwangila a wani ɓangare na shirin inganta koyarwa a cibiyoyin ilimi, da ake ce wa Niger LIRE.

Kamfanin dillancin labaran ƙasar ANP ya ruwaito cewa an yi bikin miƙa ayyukan ne a wani taro da manyan jami’an gwamnati da wakilan kamfanonin ‘yan kwangila suka halarta a jihar a ƙarshen makon jiya.

Gwamnan ya ce miƙa wuraren ayyukan ga ‘yan kwangilar wani muhimmin mataki ne wajen inganta koyarwa a makarantun Nijar da kuma aiwatar da burin gwamnatin ƙasar ƙarƙashin jagorancin Shugaba Abdourahamane Tiani na samar wa makarantun ƙasar gine-gine na zamani da suka dace da ci-gaba.

Masu AlakaTRT Afrika - Gwamnatin Nijar ta yi watsi da buƙatar karin farashin man fetur a ƙasar

Kanal-Manjo Bana Alhassane ya tuna wa kamfanoni da aka zaɓa muhimmancin aikin da aka ba su amanar yi, yana mai cewa hakan ya nuna yadda aka yarda da ƙwarewarsu.

Gwamnan ya ce ƙa’idoji uku da suka haɗa da ingancin aiki babu ƙaƙƙautawa da biyayya ga wa’adin aiki da kuma kare lafiyar ma’aikata su ne muhimman ƙa’idojin da za su tafiyar da ayyukan a duk wuraren da za a yi su.

Ya kuma ce matakai daban-daban na hukumomin da jami’an gwamnati za su tabbatar da sa ido na dindindin kan ayyukan domin tabbatar da cewa an bi ƙa’idojin ayyukan yadda ya kamata.

Daga farko, jagoran shirin Niger LIRE, Djillou Idrissa, ya ce ayyukan da ake yi a ƙarƙashin sa idon Ma’aikatar Ilimi Ta Ƙasa da Ƙuma Ci-Gaban Harshe, an tsara su ne ranar 28 ga watan Satumban shekarar 2020 da kuɗi na farko da ya kai dalar Amurka miliyan 140.

"An ƙara dala miliyan 230 ga shirin ne ranar 11 ga watan Oktoba na shekarar 2024, lamarin da ya mayar da kasafin kuɗin aikin zuwa dala miliyan 370," kamar yadda ANP ya ambato shi yana cewa.

Ya ce an riga an yi wasu ayyuka a jihar kan kuɗi na farko da aka fara bayarwa, ciki har da gyara makarantar koyar da malaman Firamare na Dosso da samar da komfutoci 213 ga hukumar ilimi ta yanki da makarantar koyar da malaman ta Dosso da kuma ababen haɗa na’urar samar da intanet ta Starlink 60 don sa ido kan makarantun firamare da sakandare.

Djillou Idrissa ya ce ƙarin kuɗin zai mayar da hankali ne kan gina ajujuwa da gine-gine masu alaƙa ciki har da ɗakunan gwaje-gwaje ga ƙanana da manyan makarantun sakandare.

Rumbun Labarai
Ethiopia da Sudan sun rufe ofisoshin jakadancin juna bayan zarge-zargen tsoma baki a yaƙin basasa
Shugaban Benin ya sauya manyan hafsoshin soji bayan kusan shekara ɗaya da yunƙurin juyin mulki
Dangote ya ƙaddamar da aikin wajen adana man fetur na dala biliyan 2.5 a Namibia
Afirka ta Kudu ta tuhumi mutum biyu saboda satar fiye da dala dubu 580 a gonar Shugaba Ramaphosa
Ghana ta ƙwato fiye da cedi biliyan 18 ta hanyar binciken kuɗi – Babbar mai binciken kuɗi
Sojojin Sudan sun ce sun dakile hare-haren RSF a yankin Kogin Nilu
Wakilan musamman na China za su ziyarci Afirka don tattaunawar zaman lafiyar yanki
Nijar ta karɓi tankokin dakon man fetur 53 daga Aljeriya domin rage matsalar karancin mai
Ayarin motocin sojin Aljeriya ya isa birnin Arlit na Nijar
Saudiyya ta dakatar da shiga kasar daga Kenya saboda Ebola
Putin ya ce Rasha ta fi Ƙasashen Yamma masu 'mulkin mallaka' zama abokiyar hulɗar gaskiya ga Afirka
Yadda nasarar Lula da Silva a zaɓen Brazil na 2026 za ta yya buɗe sabbin damarmaki ga Afirka
An kashe aƙalla Kiristoci ’yan Orthodox 60 a hare-hare a yankin Oromia na Ethiopia
Nijar ta zargi Chadi da haɗa baki da Faransa wajen kai mata hari
Tiani: Dole ne Nijar ta warware matsalolin da suka daɗe suna dabaibaye ta kafin samun nasara
Majalisar Dattawan Aljeriya ta amince da buƙatar tura sojoji zuwa Nijar
Gabon ta janye takunkumin amfani da kafafen sada zumunta bayan watanni takwas
Kenya ta tabbatar da mutuwar mutum na biyu daga cutar Ebola
Ana fargabar mutane da dama suna ƙarƙashin ɓaraguzan gini mai hawa 12 da ya rushe a Kenya
Daga Nijeriya zuwa Kenya, mutane na tsawon rai amma ba tare da cikakkiyar lafiya ba