| Hausa
DUNIYA
2 minti karatu
Faransa da Sifaniya na fama da mummunar gobarar daji
Hukumomi sun yi gargaɗin fuskantar wani dare mai wahala yayin da gobarar daji ke ƙara ƙamari, lamarin da ya tilasta kuɓutar da fiye da mutum 300,000 a faɗin Faransa da Sifaniya.
Faransa da Sifaniya na fama da mummunar gobarar daji
An ci gaba da kuɓutar da mutane da yawa yayin da gobarar dajin ke bazuwa a faɗin Faransa da Sifaniya / Reuters

Gobarar daji mai tsanani a wurare daban-daban ta tilasta wa mutum fiye da 300,000 barin muhallansu a faɗin Faransa da Sifaniya yayin da hukumomi ke ci gaba da ƙoƙarinsu na cin ƙarfin gobarar.

Hukumomi a kudu maso yammacin Faransa sun faɗaɗa umarnin ƙaura bayan wutar ta ƙara ƙamari a yankin Gironde, ciki har da wuraren Bordeaux.

Jami’ai sun ce jerin gobarar sun haddasa iska mai ƙarfi, lamarin da ya sanya wa aikin kashe gobarar ya zama mai sarƙaƙiya.

A Sifaniya ma, hukumomi sun ba da ƙarin umarnin ƙaura kusa da Toledo, a kudu maso yammacin Madrid, yayin da yanayi ya ci gaba da ruruta wutar.

Jerin gobarar biyu sun shafe kwanaki suna ci duk da gagarumin aikin kwana-kwana da ake yi.

‘Yan kwana-kwanan Faransa biyu sun mutu a Bordeaux a farkon mako, yayin da wata gobara ta daban kusa da Valencia ta kashe wani mutum ranar Asabar.

A Faransa, hukumomi sun fara kuɓutar da kimanin mutum 197,000 kusa da Bordeaux kafin su ƙyale kimanin mutum 3,000 su koma.

Daga baya an bai wa kimanin mutum 55,000 umarnin ƙaura, lamarin da ya sa adadin waɗanda aka kuɓutar daga yankin Gironde ya ɗara 200,000.

A Sifaniya, an kuɓutar da kimanin mutum 60,000 daga ƙauyukan da ke yamma da Madrid daga farkon ranar Asabar.

Daga baya hukumomi sun faɗaɗa umarnin ƙaurarsu zuwa aƙalla ƙananan hukumomi takwas a kusa da Toledo.

Faransa ta tura sojoji 1,500 da jami’an tsaro 1,700 da kuma ƙarin jiragen sama domin tallafa wa ayyukan kwana-kwana. Jami’ai sun ce kimanin ‘yan kwana-kwana 1,400 ne ke kokarin kasha gobarar.

Hukumomin Faransa sun ce jerin gobara a faɗin ƙasar sun ƙone kusan hekta 98,000. A kudu maso yammacin Faransa kawai, fiye da hekta 32,000 sun ƙone kuma aƙalla gine-gine 100 sun lalace.

Ministan tsaron cikin gidan Sifaniya ya ce jerin gobara a yammacin Madrid sun ƙone abin da ya kai hekta 25,000. Manyan gobarar daji biyu sun haɗu sun zama ɗaya kuma suna barazana ga wurare a kusa da babban birnin ƙasar.

Hukumomi a ƙasashen biyu sun sami tallafi daga Ƙungiyar Tarayyar Turai ta hanyar jirgin saman kwana-kwana da wasu ƙasashen ƙungiyar suka bayar.