| Hausa
WASANNI
2 minti karatu
EFCC ta fara binciken Hukumar kwallon kafa ta Nijeriya, NFF
Baya ga batun kashe kuɗaɗe, hukumar ta NFF tana fuskantar suka kan yadda take gudanar da harkokin ƙwallo a Nijeriya, ganin yadda tawagar Super Falcons ta gaza samun cancantar buga gasar Kofin Duniya ta mata ta FIFA 2027.
EFCC ta fara binciken Hukumar kwallon kafa ta Nijeriya, NFF
Nigeria Economic and Financial Crimes Commission EFCC

Rahotanni daga Nijeriya na cewa hukumar yaƙi da laifukan cin hanci da rashawa ta ƙasar, EFCC ta ƙaddamar da bincike kan yadda hukumar ƙwallon ƙafa ta ƙasar, NFF ta kashe wasu kuɗaɗe har naira biliyan 12 da gwamnatin tarayya ta bayar.

Kuɗaɗen na biyan albashin da bonos ɗin ‘yanwasa, shugaba Bola Tinubu ne ya amince a sakar wa NFF a 2024 don biyan basussukan da tawagogin ƙwallo ke bin hukumar.

Tuni aka gayyaci wasu jami’an NFF da ke da alaƙa da kashe kuɗaɗen suka bayyana gaban EFCC, inda suka bayar da bahasi, kafin a ba da belin su.

Ana danganta rahotannin da wata wasiƙa da wani lauya mai suna Onoja Joshua, Esq ya sanya wa hannu a madadin Babban Sakataren NFF, wadda ta ba da bayanai da aka nema game da yadda aka kashe kuɗaɗen.

A watan Janairun 2024 ne Shugaba Tinubu ya ba da izinin sakarwa NFF kuɗaɗen gabanin gasar Kofin Afirka ta AFCON 2023 da aka yi a Ivory Coast, don biyan ‘yan babbar tawagar Super Eagles da sauran tawagogin ƙwallo na ƙasa, da albashin jami’an horarwa na wata 15.

Dakatar da zaɓen NFF

Sai dai zuwa Nuwamban 2025, ‘yan tawagar Super Eagles sun ƙaurace wa atisaye a birnin Rabat na Morocco, gabanin wasan neman cancantar buga Kofin Duniya tare da Gabon, inda suka yi ƙorafi kan bashin da suke bi tun daga 2019.

Baya ga batun kashe kuɗaɗe, hukumar ta NFF tana fuskantar suka kan yadda take gudanar da harkokin ƙwallo a Nijeriya ganin yadda tawagar Super Falcons ta gaza samun cancantar buga gasar Kofin Duniya ta mata ta FIFA 2027.

Hakan ya faru ne tamkar yadda takwararta ta maza Super Eagles, ta gaza zuwa gasar FIFA 2026 da aka kammala a watan Yunin da ya gabata a Amurka, Canada, da Mexico.

Sai dai duk da wannan ƙalubale, shugaban Hukumar NFF, Ibrahim Gusau, wanda aka zaɓa a Satumban 2022 yana neman wa’adi na biyu a zaɓen da za a yi a Satumban 2027.

A halin yanzu akwai raɗe-raɗin cewa Hukumar Wasanni ta Nijeriya tana yunƙurin dakatar da zaɓen mai zuwa, domin ta kafa kwamitin da zai daidaita lamura a harkokin ƙwallon ƙafa na Nijeriya.