Harin da aka kai wa 'yan kasuwar Ghana a Burkina Faso ya sa farashin tumatur ya tashi
Farashin tumatur, wanda yawanci ana shigarwa Ghana daga ƙasar Burkina Faso, ya tashi bayan rahotannin harin da ya toshe hanyar fataucinsa da na cinikayya, in ji kamfanin dillancin labaran ƙasar.
Wani harin da ‘yanta’adda suka kai wa masu sayar da tumatur a Burkina Faso ya fara tasiri kan farashin kayayyakin miyar a wasu sassan Ghana.
Kamfanin dillancin labaran ƙasar Ghana ya ambato ‘yan kasuwa da masu sayen tumatur a kasuwannin Denu da Agbozume na Ketu South suna bayyana yadda farashin tumatur ɗin ya yi tashin gauron zabi.
Farashin tumatur, wanda yawanci ana shigarwa Ghana daga ƙasar Burkina Faso, ya tashi bayan rahotannin harin da ya toshe hanyar fataucinsa da na cinikayya, in ji kamfanin dillancin labaran ƙasar.
Wani binciken farashin kayayyakin kasuwa da kamfanin dillancin labaran ƙasar Ghana ya gudanar a Denu da Agbozume ya gano cewa kwandon tumatur da a baya ake sayarwa GHS30 yanzu ya koma GHS50 yayin da ƙaramin kwando da ake sayar da shi GHS20 ya koma GHS30 zuwa GHS35.
Masu sayar da tumatur sun alaƙanta tashin farashin da ƙarancin tumatur da kuma tsaiko a jigilar tumatur.
Wasu masu sayar da tumatur sun shaida wa kamfanin dillancin labaran Ghana cewa shigar da tumatur Ghana daga Burkina Faso ya ragu sosai tun lokacin da aka kai harin, lamarin da ya haddasa tsadarsa.