Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Nijeriya, INEC tana tunanin aiwatar da zaɓen gwaji na Shugaban Kasa gabanin zabukan shekarar 2027, domin gwada tsarin tantance masu zaɓe da tura tare da duba sakamakon zaɓe a cikin wani yanayi da ya dace da na ranar zaɓe.
Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan ne ya yi wannan bayani ranar Laraba a Abuja yayin da yake magana a taron ƙasa da ƙasa na ƙungiyar masana ilimin sadarwa da ƙwararru (ACSPN).
Amupitan, wanda wani kwamishina na hukumar Sani Adam ya gabatar da bayaninsa a taron, ya ce sahihancin tsarin zaɓen ba ya dogara ga na’urar BVAS da kuma takardun sakamako, har ma da yadda ‘yan Nijeriya suka gane da kuma yarda da bayanai game tsarin zaɓen.
Ya yi kira da a haɗa fasahar zaɓe da ta sadarwa a wuri ɗaya gabannin zaɓen 2027, yana mai gargaɗin cewa labaran ƙarya da aka kitsa da ƙirƙirarriyar basira na gagarumar barazana ga sahihancin zaɓukan.
Game da ƙarin yadda ake amfani da ƙirƙirarriyar basira wajen juya bayanai, shugaban na INEC ya ce amfani da fasahara ƙirƙrarriyar basira wajen juya bayanai ta hanyar ƙirƙiro bidiyo na ƙarya da murya ta ƙarya da hotuna sun ƙara zama masu araha kuma da wahalar ganowa.
Ya yi ishara ga yadda aka yaɗa bayanan ƙarya a zaɓukan da aka yi kwanan nan a yammaci da gabashin Afirka, ciki har da bayanai na ƙarya da ke da alaƙa da zaɓen 2023 na Nijeriya.
Amupitan ya yi gargaɗin cewa irin waɗannan ayyukan za su iya kai ga miliyoyin masu amfani da kafafan sada zumunta kafin masu bin diddigi su tabbatar da gaskiyar lamarin.
Ya ce barazanar ta wuce ƙirƙiro ƙarya kawai, yana mai cewa murɗa yadda kafafan ke aiki ta yadda za a rinƙa tura wa masu zaɓe saƙonni da ke karo da juna ba tare da wani dalili ba.


























