| Hausa
TURKIYYA
3 minti karatu
Daƙile yunƙurin juyin mulki na 2016 ya 'bayyana 'yancin kai' na ƙarni ga Turkiyya, in ji Erdogan
A wani saƙo da ya wallafa a ranar 15 ga Yuli na cika shekaru 10 da yunƙurin juyin mulki da bai yi nasara ba a Turkiyya, Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya ce Turkiyya ta fito ƙarara ta ƙara haɗin kai da jajircewa a yaƙin da take yi da FETO.
Daƙile yunƙurin juyin mulki na 2016 ya 'bayyana 'yancin kai' na ƙarni ga Turkiyya, in ji  Erdogan
Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya bayyana cewa ranar 15 ga watan Yuli babbar nasara ce ga dimokuradiyya a ƙasar

Shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya bayyana yunƙurin juyin mulki na ranar 15 ga Yuli, 2016 da bai yi nasara ba a matsayin wani muhimmin lokaci a tarihin ƙasar, inda ya kira shi a matsayin "'yancin kai" na ƙarni ga Turkiyya.

A wata muƙala mai taken 15 ga Yuli: Samun 'yancin kai na ƙarni ga Turkiyya, wadda aka wallafa don bikin cika shekaru 10 a tsarin Dimokuraɗiyya da kuma Ranar Haɗin Kan Ƙasa, Erdogan ya ce juyin mulkin da bai yi nasara ba wanda Ƙungiyar Ta'addanci ta Fetullah (FETO) ta shirya ba kawai yunƙurin kifar da gwamnati ba ne, har ma da hari ga 'yancin kai da kuma ƙudurin dimokuraɗiyya na ƙasar.

"Ranar 15 ga Yuli ba wai kawai dare ne da aka daƙile wani yunƙuri na juyin mulki mai cike da ruɗani ba, babbar nasara ce ga dimokuraɗiyya, wadda aka rubuta da haruffan zinare a tarihi, a daidai lokacin da al'ummarmu ke kare muradu, dimokuraɗiyya da kuma 'yancin kai wanda ya jawo asarar rayuka da dama," in ji shi.

An kashe mutane 253 tare da jikkata fiye da 2000

Erdogan ya ce al'ummar Turkiyya sun amsa kiransa na fitowa kan tituna da irin jajircewar da aka nuna a yaƙin neman 'yancin kai na ƙasar, inda ya ƙara da cewa an kashe mutane 253 kuma an jikkata fiye da 2000 yayin da suke adawa da yunƙurin juyin mulkin.

Ya ce kiransa ga jama'a da su nuna turjiya ya nuna ƙarfin gwiwarsa ga “hikimar dimokuraɗiyyar ƙasar, da hangen nesa, da kuma jarumtarta.”

A yayin da yake waiwaiye bayan yunƙurin juyin mulkin, Erdogan ya ce hukumomi sun bi sahun yaƙi da ƙungiyar FETO a ciki da wajen Turkiyya.

“Mun kawar da FETO daga kowane fanni, tun daga cikin gwamnati da sojoji zuwa ɓangaren shari'a da ‘yankasuwa," in ji shi, yayin da ya jaddada cewa yaƙin bai ƙare ba.

"Hanya ɗaya tilo da za a iya hana ƙungiyar FETO da ire-irenta daga yin kutse ko shiga ƙasarmu ita ce a ci gaba da rayuwa da ruhin ranar 15 ga watan Yuli tare da wayar da kan jama'a musamman al’ummar gaba, " in ji shi.

‘Turkiyya ta ƙara ƙarfi a cikin shekaru nan da suka wuce’

“Muna ci gaba da yaƙi da FETO da duk wasu ƙungiyoyin ta'addanci masu iri wannan ƙuduri. A juyayin cika shekaru 10 na ranar 15 ga Yuli, Turkiyya ta ƙara ƙarfi, tare da samun haɗin kai,” in ji shi.

“Muddin ruhin ranar 15 ga Yuli ya ci gaba da wanzuwa a wannan ƙasa, kar wani ya yi shakkar cewa shirye-shiryen maciya amana da kuma munanan matakan da waɗanda suka kitsa juyin mulkin a duniya ba za su taɓa yin nasara ba,” in ji shi.

Kazalika Shugaba Erdogan ya jinjina wa shahidan da aka kashe a lokacin yunƙurin juyin mulkin da kuma addu'ar Allah ya dawwamar da haɗin kan Turkkiyya.

Rumbun Labarai
30 ga Agusta: Nasarar da ta buɗe hanyar tasowar Turkiyya ta zamani
An haƙo wani sassaƙen ɗan'adam zaune a kan damisa mai shekaru 11,000 a Turkiyya
Turkiyya ta ƙara haɓaka kasuwancin da take yi da ƙasashen Musulmi
Aselsan: Kamfanin tsaro na Turkiyya zai baje-kolin jirgin ƙarƙashin ruwansa a bikin Teknofest
Turkiyya ta ƙaddamar da shirin 2026–2030 na zama cibiyar fasahar AI ta duniya
Trump ya yi 'murna' kan yarjejeniyar tsaro ta Makka da Turkiyya da Pakistan da kuma Saudiyya suka yi
Shugaba Erdogan ya jinjina wa shekara 25 na Jam'iyyar AK kan samar da 'sauyi mai tarihi' a Turkiyya
Shekaru 25 na Jam’iyyar AK da matsayin Turkiyya na mai taka rawa a yanki da ma duniya
Ministan Harkokin Wajen Masar ya gode wa Turkiyya saboda tarban karamci da ta yi wa Mohamed Salah
Turkiyya ta yi kira ga Tunisia da ta saki jagoran Ennahda Ghannouchi da ke tsare a kurkuku
Turkiyya ta kama mutum 30 a wani samame da aka kai kan ƙungiyar masu aikata laifuka ta Alihan
Turkiyya za ta ci gaba da taka rawa da kuma shiga tsakani a Libya, in ji Ministan Harkokin Waje
Cikin hotuna: Turkiyya ta haskaka muhimman wurare don murnar Yajejeniyar Tsaron Hadin Gwiwa ta Makka
An fara gasar baje-kolin jiragen sama marasa matuka ta TEKONOFEST a garin Sirnak na Turkiyya
Erdogan zai kai ziyara Saudiyya don tattaunawa da Mohammed bin Salman da Firaministan Pakistan
Shugaban sadarwa na Turkiyya ya ce Isra'ila na yi wa yunƙurin zaman lafiya na Gaza zagon ƙasa
Turkiyya ta kama ɗanta'addan FETO da ake nema bisa yunƙurin kashe Shugaba Erdogan a shekarar 2016
Turkiyya ta yi fice a Gasar Duniya ta Rubutu a Kwamfuta da kambi 36
Turkiyya da Nijeriya sun ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa kan ƙera jiragen ruwa
Shugaba Erdogan ya taya tawagar Sultans of Net ta Turkiyya murnar lashe gasar ƙwallon raga ta mata