| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Shugaban Hukumar Alhazan Nijeriya Sheikh Abdullahi Saleh Pakistan ya ajiye aikinsa
Kawo yanzu dai ba a bayyana dalilin murabus ɗin ba, amma kafofin watsa labaran Nijeriya sun ambato Ahmed Muazu, mai magana da yawun shugaban yana tabbatar da batun.
Shugaban Hukumar Alhazan Nijeriya Sheikh Abdullahi Saleh Pakistan ya ajiye aikinsa
Shugaban hukumar jin daɗin alhazai ta Nijeriya, Abdullahi Usman, ya ajiye aikinsa / NAHCON
18 awanni baya

Rahotanni daga Nijeriya na cewa shugaban Hukumar Alhazan Nijeriya, (NAHCON), Sheikh Abdullahi Saleh Pakistan, ya ajiye aikinsa yayin da ake shirye-shiryen aikin Hajji na 2026.

Kawo yanzu dai ba a bayyana dalilin murabus ɗin ba, amma kafofin watsa labaran Nijeriya sun ambato Ahmed Muazu, mai magana da yawun shugaban yana tabbatar da batun.

Shugaban Bola Tinubu ya naɗa Sheikh Pakistan a matsayin shugaban hukumar NAHCON a shekarar 2024 bayan ya cire Jalal Arabi daga shugabancin hukumar.

A wancan lokacin, an ƙaddamar da bincike kan Arabi bisa zargin yin ba daidai ba da kuɗin da gwamnatin tarayya ta fitar domin aikin hajji.

A shekarar 2025 ne shugaban ya jagoranci aikin Hajjinsa na farko a hukumar NAHCON.

Masu AlakaTRT Afrika - Yadda tsadar kudin Aikin Hajjin bana ke barazana ga maniyyata a Nijeriya

Sai dai shi ma shugabancin Sheikh Pakistan na cike da ce-ce-ku-ce da zarge-zarge na badaƙalar kuɗi.

Ce-ce-ku-cen sun ta’allaƙa ne kan zarge-zargen hallata kuɗaɗen haram a lokacin aikin hajjin shekarar 2025 —iƙirarin da ya ruruta wutar rikicin cikin hukumar kuma ya janyo hankalin jama’a kanta.

A watan Janairun shekarar 2026, rikicin ya yi ƙamari a lokacin da rahotanni suka ce kwamishinonin hukumar NAHCON sun gabatar da takardar ƙorafi ga Shugaba Tinubu, inda suka nuna rashin amincewa da shugabancin Sheikh Pakistan. Takardar ƙorafin ta zargi shugaban hukumar da gazawa wajen shugabanci da kuma rashin iya gudanarwa, lamarin da ya daɗa ta’azzara rikicin cikin hukumar.

Wannan yanayin ya sa mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ya shiga lamarin, inda ya kira taro na musamman na masu-ruwa-da-tsaki kimanin mako biyu da suka gabata domin ƙoƙarin sasanta tsakanin ɓangarorin da kuma dawo da zaman lafiya cikin hukumar ta NAHCON.