Bankin Duniya ya amince da bayar da tallafin dala miliyan 250 domin taimakawa wajen farfado da ɓangaren kuɗi a Nijar tare da inganta damar samun jari ga ƙanana da matsakaitan sana’o’i.
Tallafin, wanda aka amince da shi a ranar 12 ga Maris na 2026, ya fito ne daga International Development Association wadda ke ƙarƙashin Bankin Duniya, kuma ana sa ran tallafi zai taimaka wajen dawo da isassun kudi a bankuna tare da ƙarfafa bankuna su sake bai wa ƙanana da matsakaitan ‘yan kasuwa bashi a faɗin kasar.
A cewar Bankin Duniya, shirin zai taimaka wa cibiyoyin kudi su ci gaba da bayar da rance ga ‘yan kasuwa sannan ya kuma taimaka wajen samar da ayyukan yi da ƙarin hanyoyin samun kuɗin shiga ga jama’a.
Tattaunawa kan wannan shiri ta ɗauki watanni da dama, kuma an sake duba ta a ƙarshen watan Janairu a yayin ganawar Firaministan Nijar, Ali Mahamane Lamine Zeine, da wata tawaga daga Bankin Duniya karkashin jagorancin wakilin bankin a Nijar, Affouda Léon Biaou.
Ana sa ran shirin zai taimaka wa kimanin ƙanana da matsakaitan sana’o’i 7,500, ciki har da kasuwancin da mata ke jagoranta da kuma ayyukan da ke jure sauyin yanayi, tare da taimakawa wajen ƙirƙira ko kuma ci gaba da riƙe kusan ayyukan yi 58,000.
Bangaren kuɗi na Nijar ya fuskanci matsin lamba tun bayan rikicin siyasa na watan Yulin 2023, wanda ya janyo takunkumin tattalin arziki daga ƙasashen yankin, lamarin da ya jefa bankuna da cibiyoyin bada rancen kuɗi cikin matsalar rashin isasshun kudi.
Bankin Duniya ya ce wannan matsala ta rage ƙarfin bankuna wajen bai wa ‘yan kasuwa rance, musamman ƙanana da matsakaitan sana’o’i da ke buƙatar jari domin ci gaba da gudanar da harkokinsu da bunkasa kasuwanci.
Jami’in ayyuka na Bankin Duniya a Nijar, Johan A. Mistiaen, ya ce shirin zai taimaka wajen buɗe sabbin damammaki ga ‘yan kasuwar Nijar.
Shirin zai kuma hada da taimakon fasaha ga cibiyoyin kuɗi da kuma wani shiri na gaggawa domin ba da damar ɗaukar matakan hanzari idan wata matsala ta sake tasowa nan gaba.












