Masarautar Kano da ke arewacin Nijeriya ta yi watsi da wani bidiyo da ya yaɗu a kafafen sada zumunta, wanda ke iƙirarin cewa Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na II, ya samu kari-oba a ɗaya daga cikin darussan Shari’a da yake karatun digiri a kai a Jami’ar Northwest da ke Kano, kamar yadda kafofin watsa labaran ƙasar suka ruwaito.
Bidiyon, wanda ya bazu sosai a ranar Lahadi, ya yi zargin cewa tsohon Gwamnan Babban Bankin Nijeriyar bai cika ƙa’idar cin nasarar ɗaya daga cikin darussansa ba.
A halin yanzu, Sarki Sanusi ɗalibi ne a mataki a ji biyu na sashen digirin shari’a a jami’ar.
Sai dai Sakataren Ofishin Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammad Ado, ya bayyana cewa zargin ba gaskiya ba ne, yana mai cewa Sarkin na ci gaba da tafiyar da karatunsa yadda ya kamata da burin kammala jami’ar da digiri mafi daraja (First Class).
A cewarsa, bayanan da Masarautar ke da su sun nuna cewa Sarkin na buƙatar maki ɗaya kacal domin cim ma matakin maki mafi daraja, kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

“Mun halarci wani shiri da ɗaliban shari’a suka shirya a jami’ar a ranar Asabar, kuma wani ɗalibi ne ya ɗauki bidiyon. Amma abin da ake yaɗawa ba gaskiya ba ne.
“A lissafinmu, maki ɗaya ne kawai ya rage wa Mai Martaba domin ya samu First Class. Sunday Dare ne ya halarci shirin a matsayin baƙon malami,” in ji Ado.
Shi ma wani ɗalibin jami’ar, Ibrahim Abubakar-Danmasani, ya musanta wannan iƙirari, yana mai cewa har zuwa ranar Lahadi ba a fara jarrabawar jami’ar ba.
Ya ce an tsara fara jarrabawar ne a ranar Litinin.
Majiyoyi daga cikin jami’ar su ma sun tabbatar da bayanin Masarautar, suna cewa bidiyon da ya yaɗu ba ya nuna ainihin matsayin karatun Sarkin Kano.
Sun ƙara da cewa wasu matasa ne suka ɗauki tare da yaɗa bidiyon a matsayin wasa, abin da daga baya ya rikide ya zama jita-jita a kafafen sada zumunta.





















