| Hausa
GABAS TA TSAKIYA
2 minti karatu
Trump ya ce bai kamata Iran ta samu makamin nukiliya ba a liyafar da aka shirya wa Sarki Charles III
Shugaban Amurka ya ce Sarki Charles "ya yarda da [maganata]" cewa bai kamata Tehran ta iya mallakar makamin nukiliya ba, yana mai jaddada cewa sun yi nasara a kan ƙasar ta hanyar soji.
Trump ya ce bai kamata Iran ta samu makamin nukiliya ba a liyafar da aka shirya wa Sarki Charles III
A cikin kalamansa bayan Trump, Charles bai yi magana game da Iran ko yaƙin ba. / Reuters

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce Sarkin Birtaniya Sarki Charles III ya yarda da ra’ayinsa cewa bai kamata Iran ta mallaki makamin nukiliya ba, inda ya sako batun rikicin Gabas ta Tsakiya cikin kalamansa a wata liyafar maraba da aka shirya wa basaraken a Fadar White House.

An yi taron ne ranar Talata, a rana ta biyu ta ziyarar Sarkin ta kwanaki huɗu zuwa Amurka.

"Muna wani aiki kaɗan a Gabas ta Tsakiya a halin yanzu, kuma muna yinsa da kyau," kamar yadda Trump ya bayyana a liyafar.

"Mun yi nasara ta soji kan waccar abokiyar gaban, kuma ba za mu taɓa bari wannan abokiyar gaban ta taɓa — Charles ya amince da [ra’ayina] fiye da ni ma — ba za mu taɓa ƙyale wannan abokiyar gaban ta mallaki makamin nukiliya ba."

A kalamansa bayan na Trump, Charles bai yi magana game da Iran ko yaƙin ba.

A wani jawabin da ya yi wa majalisar dokokin Amurka, Charles bai yi magana game da yaƙin Iran ba.

Masu AlakaTRT Afrika - Trump bai yarda da tayin Iran na sake buɗe Mashigar ruwan Hormuz ba, in ji rahotanni

Basaraken na Birtaniya ya bayyana muhimmancin ci-gaba da samun tallafin Amurka a yaƙin da Ukraine ke yi da Rasha da kuma hatsarin keɓancewa daga sauran ƙasashen duniya.

Birtaniya da Amurka sun shafe shekaru suna cewa bai kamata Tehra ta haɗa makamin nukiliya ba.

Tehran ta musanta cewa tana neman makaman na nukiliya amma ta ce tana da ‘yancin gina fasahar nukiliya domin buƙatu na zaman lafiya, ciki har da sarrafa yuraniyom, a matsayinta ta ƙasar da ta sa hannu a yarjejeniyar hana yaɗuwar makamin nukiliya.

Amurka da Isra’ila sun ƙaddamar da yaƙi kan Iran ranar 28 ga watan Fabrairu. Tehran ta mayar da martani da hare-hare kan abin da ta bayyana matsayin kayayyakin Amurka a yankin, da yawa daga cikinsu a cikin ƙasashen Larabawa da ke gaɓar teku ne.

An ayyana tsagaita wuta ranar 8 ga watan Afrilu ta hanyar masu shiga tsakani na Pakistan, kuma tattaunawa ta biyo baya a Islamabad tsakanin ranar 11 zuwa 12 ga watan Afrilu , amma tattaunawar ta ƙare ba tare da cim ma matsaya ba .

Daga baya sai Trump ya ce an tsawaita tsagaita wutan bisa buƙatar Pakistan kafin Tehran ta gabatar da shawarwari.