Wane ne Franck Biya da ake hasashen zai iya Shugaban Ƙasar Kamaru na gaba?
Ana ci gaba da muhawara a tsakanin 'yan Kamaru game da yiwuwar samun sauyin shugabanci daga Biya babba zuwa Biya ƙarami da kuma tasirin da hakan zai haifar.
Batun siyasa da shugabancin Kamaru sun sake janyo zazzafar muhara.
Suna ɗaya da ake yawan ambatowa a kafafen yada labarai shi ne Franck Emmanuel Biya, wato ɗan shugaban ƙasar Paul Biya da ya daɗe a kan mulki.
A 'yan kwanakin nan, kafafen yada labarai daban-daban na gida a ƙasashen Afirka, ciki har da na Kamaru, sun ba da rahoton cewa an naɗa Franck a matsayin mataimakin shugaban ƙasar kana shi zai gaji mahaifinsa a matsayin shugaban ƙasar na gaba.
Rahotannin, waɗanɗa suka nakalto wani kwafin umarnin shugaban kasa da aka fitar mai ɗauke da kwanan 4 ga watan Afrilun 2026, sun ce Franck zai jagorancin shugabancin rundunar sojin kasar tare da yin aiki a matsayin "Wakilin Minista" a Ma'aikatar Tsaro.
Kawo yanzu dai gwamnatin Kamaru ba ta tabbatar ko musanta rahotannin kafofin watsa labarai da aka yaɗa ba.
An dawo da kujerar mataimakin Shugaban Ƙasa
Majalisar Dokokin Ƙasar ta dawo da kujerar mataimakin shugaban ƙasa a makon da ya gabata, bayan shafe fiye da shekaru 50 da soke matsayin.
Dokar da ta dawo da matsayin ta tanadi cewa mataimakin shugaban ƙasa zai zama shugaban ƙasa kai tsaye idan shugaban ya mutu, ko ya yi murabus ko kuma ya rasa ƙarfinsa har abada.
Yayin da wasu masu sharhi ke cewa, akwai yiwuwar dokar an kafa ta ne a matsayin wata dabara ta tabbatar da cewa mataimakin da Paul Biya ya zaɓa shi zai gaje shi, matakin da jami'an gwamnati suka ce yana da nufin tabbatar da "tsaron cigaban gwamnati".
Paul Biya wanda ya hau mulki tun daga shekarar 1982, a halin yanzu shi ne shugaban ƙasa mafi tsufa a kan mulki a duniya yana da shekaru 93 kuma a wa’adin mulkinsa na takwas bayan zaɓen shugaban ƙasa na watan Oktoba.
Ɗansa, Franck Emmanuel Biya, wanda yana cikin waɗanda ake hasashen za su iya maye gurbinsa, ba a cika jin duriyarsa ba a tsawon shekaru, haka kuma ba a saba ganinsa a cikin harkokin siyasa ko mukamai na gwamnati ba.
Ɗankasuwa ne. An haife shi a 1971, kuma Franck shi ne babban ɗan Shugaba Paul Biya.
Mahaifiyarsa ita ce Jean-Irène Biya, matar Shugaba Biya ta farko, wacce ta mutu a shekarar 1992.
Franck ya yi karatu a Kamaru kafin ya koma Amurka, inda ya kammala karatunsa na digiri a fannin Kimiyyar Siyasa da Tattalin Arziki daga Jami'ar Kudancin California a shekarar 1994.
Sannan ya yi aiki a Bankin Kasashen yankin Tsakiyar Afirka sannan daga baya ya yi aiki a wani kamfanin gandun daji.
A shekarar 2004, ya kafa Venture Capital PLC, wani kamfani da ke dake gudanar da harkokin banki da gandun daji da kuma makamashi, inda ya mai da hankali a hannayen jari a Afirka da wasu ƙasashen waje.
Yayin da ake kan jiran sanarwa a hukumance game da nadin mataimakin shugaban ƙasa a Kamaru, ana ci gaba da muhawa a tsakanin 'yan ƙasar Kamaru game da yiwuwar sauyin shugabanci daga Biya babba zuwa Biya ƙarami da kuma tasirin da hakan zai haifar.