| Hausa
AFIRKA
2 minti karatu
Ghana ta amince da ɗaurin shekara 20 ga duk wanda ya mayar da gonar koko zuwa wani abu daban
Hukumomi sun ce dokar za ta bai wa dukkan gonakin koko kariya, lamarin da zai mayar da yin wani abu daban da gonakin koko laifi.
Ghana ta amince da ɗaurin shekara 20 ga duk wanda ya mayar da gonar koko zuwa wani abu daban
Tsohon Hoto: Za a ƙaƙaba gagarumar tara kan ko wace bishiyar koko da juya akalar gonar kokon ya shafa, in ji dokar

Majalisar dokokin Ghana ta amince da ƙudirin dokar da zai iya sa a yi wa manoman koko ɗaurin shekaru 20 idan suka mayar da gonakinsu wani abu daban da ya saɓa wa abin da gwamnati ta ba su damar yi a wajen.

An amince da sabon ƙudirin ne ranar Alhamis, amma ba a bayyana cikakken abin da dokar ta ƙunsa ba har zuwa yammacin Lahadi. Shugaba John Mahama bai rattaɓa hanu kan dokar ba tukunna.

Dokar za ta bai wa dukkan gonakin koko wani matsayi na kariya, abin da zai mayar da yin wani abu daban a gonar koko ba tare da samun izinin hukuma ba zuwa aikata laifi, lamarin da ya janyo suka daga manoma.

Hukuncin dokar dai zai kuma mayar da hankali kan haƙar zinari ba bisa ƙa’ida ba, inda za a yi ɗaurin da ya kai na shekara 10 zuwa 20 da kuma tara mai yawa kan dukkan wata bishiyar koko da aka sare.

Ɗaruruwan dubban manoma a Yammacin Afirka sun dogara ne kan noma domin samun kuɗaɗen shiga na tafiyar da rayuwarsu. A ƙasar Ivory Coast mai maƙwabtaka, fitar da koko na samar da kashi 40 cikin 100 na abin da ƙasar ke samu daga abin da take fitarwa. A Ghana, koko da ake fitar wa na samar da kusan kaso 15 cikin 100 na kuɗaɗen ƙasashen waje.

Hukumomin gwamnati masu sa ido suna tsayar da farashin koko a farkon kowane lokacin shuka, kuma ana sayar wa ‘yankasuwar da gwamnati ta bai wa lasisi mafi yawancin kokon don kare manoma daga yawan sauyawar farashi a ƙasuwar ƙasa da ƙasa.

Sai dai kuma, bayan an samu gagarumin tashin farashin koko a kasuwannin duniya a shekarar 2024, farashin ko wane tan ɗin kokon ya kai $12,000, wanda shi ne mafi yawa a cikin shekaru da dama. Farashin ya faɗi sosai zuwa kimanin $4,000 yayin da kokon da ake samarwa ya zarce kokon da ake buƙata.