Iran ta ce ta kai hari a wurare aƙalla 500 na Isra'ila da Amurka
Kafofin watsa labaran Amurka sun ambato hedkwatar rundunar sojin Amurka ta ƙasashen ƙetare tana cewa jami'an sojin Amurka 18 ne suka ji munanan raunuka tun lokacin da Amurka da Isra'ila suka ƙaddamar da hare-hare kan Tehran.
Hare-haren ramuwar gayyar Iran sun afka wa wurare 500 da ke da alaƙa da Isra’ila da Amurka da Gabas Ta Tsakiya, kamar yadda Rundunar Juyin Juya halin Iran ta bayyana a rana ta uku ta yaƙin.
"Tun da aka fara yaƙin, jaruman dakarun rundunar sojin Iran sun kai hari kan muhimman wurare 60 da kuma wurare 500 na sojin Amurka da kuma na gwamnatin masu kaifin kishin kafa Isra’ila," in ji rundunar Juyin Juya Halin a wata sanarwar da ta fitar ranar Litinin.
Ta ƙara da cewa sun ƙaddamar da hare-hare na jirage marasa matuƙa fiye da 700 da kuma ɗaruruwan makamai masu linzami.
Tehran ta ƙaddamar da jerin hare-hare na makamai masu linzami da jirage mara matuƙa a matsayin ramuwar gayya ga hare-haren haɗin gwiwa da Amurka da Isra’ila suka kai wa Iran waɗanda aka fara ranar 28 ga watan Fabrariru, inda suka kashe jagoran addinin ƙasar Ali Khamenei tare da afka wa wasu wurare.
Wasu hare-haren Iran sun afka wa Isra’ila kai-tsaye, lamarin da ya janyo mutuwar aƙalla mutum 11 (cikin har da abin da ya faru a tsakiyar Isra’ila kamar a Beit Shemesh da kuma kusa da Birnin Ƙudus) inda wasu suka jikkata.
Iran ta kuma kai hare-hare kan wasu wuraren sojin Amurka da sansanonin sojinta a yankin, lamarin da ya kashe aƙalla jam’ian sojin Amurka huɗu tare da jikkata wasu.
Ƙasashen Larabawa da ke da sansanonin sojin Amurka irin su Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da Kuwait da Qatar da Bahrain da Saudiyya da kuma Oman sun fuskanci hare-haren makamai masu linzami na Iran kai-tsaye da kuma hare-haren jirage marasa matuƙa kan wuraren soji da na fararen-hula da na ababen more rayuwa.
Hedkwatar rundunar sojin Amurka ta ƙetare (CENTCOM) ta bayyana ranar Litinin cewa jam’ian sojin Amurka 18 ne suka “ji raunuka masu muni” tun lokacin da aka fara hare-haren haiɗn gwiwa na Amurka da Isra’ila kan Iran, kamar yadda kafar CNN ta ruwaito.
Wannan ƙarin bayanin da mai magana da yawun hedkwatar tsaron Amurkan kyaftin Tim Hawkins ya biyo bayan tabbatar da mutuwa ta huɗu da ta shafi wani jami’in sojin Amurka da ya mutu sakamakon raunin da ya ji yayin jerin hare-haren farko da Iran ta ƙaddamar a matsayin ramuwar gayya.
Aƙalla mutum 555 ne aka kashe a faɗin Iran a hare-haren haɗin gwiwa na Amurka da Isra’ila kan ƙananan hukumomin 131 kawo yanzu, in ji ƙungiyar ba da agajin gaggawa ta Red Crescent .
Hari mafi muni ya faru ne a a birnin Minab na kudu maso gabashin Iran, inda wani hari kan makarantar yara mata ƙanana ya kashe yara aƙalla 180.